Labarai

Nigeria: Malala ta nemi a sanya dokar ta baci a harkar ilimi

Mai fafatukar ‘yan cin karatun mata, Malala Yousafzai ta nemi gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta baci a fagen ilimin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato alkaluman gwamnatin kasar na cewa kimanin yara miliyan biyar da suka isa fara makarantun firamari ba sa makaranta.

 

Da take jawabi ga manema labarai a Abuja, Malala ta ce dole a bayyana kudaden da gwamnatoci a matakin tarayya da na jiha ke kashe wa kan ilimi.

Malala mai rike da kyautar Nobel wadda ta yi suna bayan ‘yan Taliban sun harbe ta a shekarar 2012, tana ziyara ne a Najeriya.

Ta gana da wasu daga cikin ‘yan Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a shekarar 2014.

Ta yi kira da a ceto sauran mata 100 da aka yi imanin cewar kungiyar na ci gaba da garkuwa da su.

Wannan ba shi ne karon farko da Malala za ta fara zuwa Najeriya ba ko kuma ta nemi a saki ‘yan matan Chibok ba.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.