Wata kotu a jihar Kanon Najeriya ta tura fitaccen mawakin Hausa Sadiq Zazzabi gidan kaso saboda wata sabuwar waka da ya fitar.
Shugaban hukumar ba da izinin wallafa fina-finai da wakoki ta jihar Kano, Ismaila Afakallahu, ya tabbatar wa jaridar Premium Times cewar mawakin mai suna Sadiq Zazzabi zai yi zaman kaso zuwa ranar Juma’a.
Hukumar ta ce duk da cewar mawakin ya gabatar da wakar gareta domin a bashi izinin wallafawa, bai jira a bashi izinin ba kafin ya kaddamar da ita.
Amma shi mawakin ya ce ana hakon shi ne saboda yana goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso.
An dade ana samun takun-saka tsakanin tsohon gwamnan da gwamna mai ci yanzu a jihar Kano.
Add Comment