Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, kwastam, ta ce ta kama manyan motoci na alfarma 37 da aka shigo da su daga kasashen ketare.
Hukumar ta sanar da wannan labari ne a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Talata, a birnin Ikko na jihar Lagos da ke kudancin kasar, inda ta ce motocin da ta kama din kirar jip ne.
Ta kara da cewa, ta kuma kama buhun shinkafa 12,000 da aka shigo da ita daga ta haramtacciyar hanya.
Hukumar ta kuma kama ganyen wiwi sama da buhu 40.
Kudinsu wadannan kayayyaki dai sun kai naira biliyan daya da naira miliyan dari shida.
Ba wannan ne karo na farko da hukumar take irin wannan kamu ba, na kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin kasar.
Hukumar ta ce nan gaba za a hana shigo da shinkafa Naijeriya.
Ta kuma ce an kama wasu da ake zargi da shigo da shinkafar da motocin.
Dama a watan Maris din 2016 ne hukumar ta sake haramta shiga da shinkifa kasar ta iyakokin da ba na ruwa ba, sakamakon ganowa da ta yi cewa kudin shigarta bai kai yadda ake bukata ba saboda fasa-kwaurin shinkafa da ake yi.
Hukumar kuma ta kan kama motocin da ake shigo da su ne saboda kin biya musu kudin harajin shigo da su da ake yi.
Sai dai dama shigo da kayayyaki irin su koken da wiwi haramun ne a dokar kasar.
An kama buhun tabar wiwi 40
Add Comment