Hukumomi a Najeriya sun ce sun gano wani gida a jihar Kano wanda suke zargin na ‘yan kungiyar Boko Haram ne, bayan wani farmakin da jami’an tsaro suka kai ranar Asabar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Rabiu Yusuf, ya ce an kai samamen ne da misalin karfe biyu na dare bayan jami’ansu sun kama wasu mutum biyu a kan hanya da harsashin bindiga.
Daga nan ne, sai ‘yan sanda suka je bincike gidan da mutanen suke zaune a Gayawa da ke karamar hukumar Ungogo.
6
Ya ce bayan sun isa gidan ne sai “aka fara musayar harbe-harbe tsakanin jami’ansa da kuma wani mutum da aka samu a gidan.
Mun yi nasarar kama mutum biyar – uku maza, biyu mata.”
Sai dai ya ce daya daga ciki ya tsere.
Kuma ya ce wanda ya tseren wani tsohon sojan saman kasar ne da aka sallama daga aiki.
Jami’an ‘yan sanda uku ne suka jikkata sanadiyyar abubuwan fashewa da mutumin ya rika jefa musu yayin da yake kokarin tserewa, kamar yadda kwamishinan ya shaida mana ta waya.
Hakazalika kwamishinan ya ce daya cikin mutane biyar din da suke hannunsu ya rasu.
Ya ce sun samu kayayyaki a gidan wadanda suka hada bindiga da harsasai da kakin sojan sama da takalman soja da na’urar kwamfuta da sauransu.
Wayannan mata suma suna cikinsu
Allah ya kara tona asirinsu
Add Comment