Labarai

Nigeria: EFCC ta kwato 'naira biliyan 329 daga kamfanonin mai'

An dade ana zargin cewar ana tafka almundahana a harkar man Najeriya inda kasar ta fi samun kudaden shiga

Hukumar yaki da cin hanci da rshawa ta Najeriya EFCC, ta ce ta kwato kimanin naira biliyan 329 ($1.4 biliyan) da wasu kamfanonin mai suka karkatar tare da hadin gwiwar kamfanin mai na kasa na NNPC.

Wata sanarwar da ta fitar ta kara da cewar an kwato kudaden ne tsakanin Yulin 2016 zuwa watan Yulin 2017 bayan wani korafi da ta samu kan zargin aikata ba daidai ba.
 
Hukumar ta ce bincike ya nuna cewar kamfanonin sun karbi mai da yawa daga gwamanti ba tare da biyan kudi yadda ya kamata ba.
Sanarwar ta ambato mai magana da yawun hukumar, Wilson Owujaren, yana cewar kamfanonin man sun hada da NNPC da Conoil Plc da Total Plc da OVH Energy da Oando Plc da Forte Oil and Gas da MRS Oil Plc da kuma NIPCO Oil Plc.
Kawo yanzu babu daya daga cikin kamfanin da ya ca uffan game da sanarwar ta EFCC.
An dade ana zargin cewar ana tafka almundahana a harkar man Najeriya inda kasar ta fi samun kudaden shiga.
Kakakin EFCC din ya ce takardar koken da aka tura wa hukumar EFCC ta yi zargin cewar kamfanonin da ke sayar da man sun yi sama da fadi da naira biliyan 40 tare da shugabannin NNPC.
Daga nan ne aka mika batun ga wata runduna ta musamman wadda ta gudanar da bincike a cikin sirri, in ji Mista Owujaren.
Ya kara da cewa bayanan da jami’anmu suka samu sun nuna cewar gwamnatin tarayya na bin kamfanonin man bashin naira biliyan 91.5 tsakanin 2010 zuwa 2016.
“Da aka zurfafa bincike kan zargin, sai aka gano cewar kamfanonin na ci gaba da karbar mai daga gwamnati ba tare da biyan kudi kamar yadda dokokin bashi na NNPC/PPMC suka tanada ba.
Karin bincike kan wannan ya sa an ganon naira biliyan 258.9,” in ji kakakin na EFCC.
Mista Uwujaren ya yi bayanin cewa jumullar bashin ta tsaya ne kan naira biliyan 349.8.
Wannan ne ya sa kawo yanzu bashin da ya yi saura ya kasance naira biliyan 20.7.
Wadannan kamfanoni na yin huldar kasuwanci dadab daban na kamfanin NNPC, ciki har da yi masa dillancin danyan mai da kuma batun shigo da tataccen man fetur kasar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.