Labarai

Nigeria: 2Face na tallafa wa 'yan gudun hijra

Kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya na kokarin taimakawa ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu

Fitaccen mawakin nan dan Najeriya da aka fi sani da 2Face Idibia na shirya wasanni waka da rawa na dandali domin tara kudaden da za a bai wa ‘yan gudun hijra a kasar.

Kasancewarsa mawakin da ya shahara a kasar, a duk inda yake wasa jama’a na yin dafifi tare da sayen tikitin shiga kallonsa.
Ana yin amfani da kudaden da aka samu wajen tallafa wa wadanda suka bar gidajensu sakamakon bala’o’in da suka same su.
 
Da yammacin ranar Asabar ne aka yi irin wannan bikin mawaka a Abuja babban birnin Najeriya, a inda mawaka da dama suka cashe.
Kididdiga ta nuna cewa akwai kimanin mutum miliyan biyu da ke gudun hijra a Najeriya.
Kuma an hakikance cewa rikicin Boko Haram ne babban abun da ya raba mutanen da gidajensu.
Tun dai shekarar 2009 ne rikicin na Boko Haram ya fara kamari musamman a arewa maso gabashin kasar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.