Masu Yiwa Kasa Hidima A Niger Za Su More Tallafin Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin jihar Niger ta yi ikirarin yin amfanin da wani kaso na tallafin kudaden da ta samu daga gwamnatin tarayya wajen inganta jin dadin masu yi wa kasa hudina wato NYSC wadanda aka turo jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Malam Ibrahim Isa Ladan ya ce gwamnatin jihar ta yi alkawarin bayar da alawus na Naira dubu biyar a kowace wata ga masu yi wa kasa hidima inda ya nemi a canja tsarin shirin ta yadda masu yi wa kasa hidimar za su koyi sana’o’in dogaro da kai da zarar sun kammala shirin.
Add Comment