-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Ni Na Koyawa Yariman Saudiyya Turanci, In ji Ma’akacin BBC


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ma’aikacin BBC Rachid Sekkai wanda ya koyar da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman Turanci a lokacin yana karami ya bayyana irin rayuwar da yariman ya rika gudanarwa ta dan gidan sarautar Saudiyya duk da cewa a lokacin ba a san shi ba sosai.

Lokacin ina koyarwa ne a makarantar Al-Anjal da ke birnin Jeddah a shekarar 1996, sai kawai aka kira ni.

Gwamnan Riyadh Yarima Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya koma birnin Jeddah da iyalansa na wani lokaci, kuma yana bukatar malamin da zai koya masu turancin Ingilishi.

Mutumin da zai zama sarkin Saudiyya daga baya ya tuntubi makarantar da nake koyarwa, kuma babu bata lokaci sai aka tura ni zuwa fadar yariman domin in fara koyar sa ‘ya’yansa da matarsa ta farko ta haifar masa: Yarima Turki da Yarima Nayef da Yarima Khalid da kuma Yarima Mohammed.

A lokacin gidana na wata unguwa mai tasowa.

Kullum da misalin karfe 7 na safe akan aika wani direba ya kai ni makarantarmu ta Al-Anjal, inda bayan an kammala karatu da misalin karfe 1 na rana sai direban ya kai ni fada.

Rachid Sekkai
Image captionHoton Rachid Sekkai a gaban makarantar Al-Anjal dake birnin Jeddah

Da zarar an wuce kofar fadar da dakaru ke gadinta, motar da ta dauko ni kan wuce ciki ta gaban wasu maka-makan gidajen kawa da ma’aikata sanye da fararen kayan aiki ke lura da su.

Akwai kuma motocin kawa masu yawa da aka ajiye su a gaban gidajen. Wannan ne lokacin da na ga motar nan mai suna Cadillac mai launin ruwan goro a karon farko.

Bayan isa cikin fadar, sai sarkin fada a lokacin – Mansoor El-Shahry wanda da alama Yarima Mohammed mai shekara 11 da haihuwa a wancan zamanin ka matukar so ya yi min iso.

Rediyon oba-oba

Na kuma lura cewa Yarima Mohammed ya fi mayar da hankalinsa ga wasa da masu gadin fada a maimakon koyon darussan da nake koya masa. babu mai tsawata masa tun da shi ne babban yaya ga ‘yan uwansa.

Na kan sami natsuwar sauran kannin Yarima Mohammed ne idan ba ya nan. Amma da zarar ya isa dakin karatun sai komai ya watse.

Ba na mantawa da yadda yake amfani da rediyon oba-oba da ya karaba hannun daya daga cikin masu gadin fada a lokacin da nake bayar da darussa.

Ya kan yi amfani da shi yana wasa da wasu masu gadin, kana yana yi min shegantaka a gaban kannensa.

Saudi Arabia's Prince Salman bin Abdul Aziz, Governor of Riyadh Region, addresses media 05 December 1986 in Paris while he presents an exhibition on the city of Riyadh at Paris Grand PalaisHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMahaifin Yarima MBS, wanda shi ne sarkin Saudiyya a yanzu, shi ne gwamnan Riyadh a lokacin da Rachid ya zama malamin ‘ya’yan nasa

A yau Yarima Mohammed mai shekara 33 shi ne ministan tsaron Saudiyya, kuma shi ne yarima mai jiran gado.

Tun bayan da ya zama mutumin da ke iko da daular ta saudiyya a bara, MBS ya yi kokarin nuna kansa a matsayin wanda ke son zamanantar da daular.

Duk da ya fuskanci turjiy adaga wasu malaman addini, ya jagoranci wasu sauye-sauyen tattalin arziki da kasar ke bukata matuka.

Ya kuma kaddamar da wani shiri na sauya alkiblar rayuwar daular mai wa al’ada kwakwaran riko.

Duk da cewa ya sami yabo daga wasu jama’a saboda gayare-gyaren da ya ke yi kasar, amma ya sha suka matuka saboda yadda Saudiyyar ke take hakkin bil Adama.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 657

- Advertisement -

Yakin da kasar ke yi a Yeman da kisan da aka yi wa dan jaridar nana dan asalin kasar Saudiyya Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyyar da ke Turkiyya a watan Oktoba na cikin manyan batutuwan da aka soke shi a kai.

Protest against Mohammed Bin Salman in Tunis (27/11/18)Hakkin mallakar hotoEPA
Image captionMohammed Bin Salman ya fuskanci kakkausar suka daga kasashen wajen saboda halayyara Saudiyya

Saudiyya ta tuhumi mutum 11 da laifin kisan dan jaridan amma ta musanta cewa Yarima Mohammed na da hannu wajen bayar da umarnin a halaka shi

Akwai lokacin da nayi mamaki – da Mohammed din ya sanar da ni cewa mahaifiyarsa ta ce wai “nayi kama da kamilin mutum”.

Ba zan iya tunawa da wani lokaci da na taba ganinta ba – a Saudiyya, matan sarakai ba sa bayyana kansu ga baki – kuma mace daya kawai na taba gani, ita ce wata mai aiki daga kasar Filifins.

Ban lura cewa ana kallo na ta wata na’ura mai daukar hoto ta CCTV ba, har sai da yariman ya nuna min wasu na’urorin a bango.

Daga nan ne sai na mayar da hankali na ga koyar da darussa ga yaran.

Ba da dadewa ba sai na shaku da Yarima Mohammed da kannensa. Duk da cewa ina koyar da ‘ya’yan gidan sarauta ne, amma ba su bambanta da sauran dalibaina na makaranta ba domin su ma masu son koyo ne amma kuma sun faye son wasa.

Tuntuben da nayi

Wata rana sai sarkin gidan fadar Mansoor El-Shahry ya kira ni, kuma ya bukaci in gana da Salman kafin ya dare karagar mulkin kasar.

Ya tambaye ni game da cigaban da ‘ya’yan nasa ke samu a fagen karatu. Sai na yi tsammanin wannan dama ce ta sanar da shi halayyar wasa da Yarima Mohammed ke da shi.

Sai na tsaya a wajen ofishin Yarima Salman, tare da sauran malaman ‘yan gidan sarautar wadanda suka fi ni sanin yadda rayuwar fada take.

Da ya fito sai dukkan malaman suka mike tsaye nan take, kuma sai nayi mamakin yadda su kayi layi suna risina masa daya bayan daya kana suna sumbatar hannunsa sannan suna sanar da shi halin ilimin yaran nasa ke ciki, sannan su wuce cikin hanzari.

President Donald Trump (L) greets The Saudi Ambassador to the United States Prince Khalid bin Salman bin Abdulaziz during an Iftar dinner in the State Dining Room at the White House 6 June 2018 in Washington DCHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionRachid ya kuma koyar da Yarima Khalid Bin Salman, wanda yanzu shi ne jakadan Saudiyya a Amurka

Da aka zo kai na, sai na kasa bin slonsu na risina masa. Ban taba yin haka ga kowan mahalulki ba. Sai kawai na mika hannuna na gaisa da shi da riko mai karfi.

Ba zan manta da yadda ya nuna al’ajabinsa ba: amma bai nuna damuwa ba ga wannan hali da na nuna.

Amma ban sanar da shi halayyar Yarima Mohammed ba domin na riga na yanke shawarar daina koyarwa domin ina son komawa Birtaniya.

Ba a dade ba sai Mista El-Shahry ya same ni inda yayi min kaca-kaca saboda kin bin tsarin girmama saraki da ban yi ba.

Ban da Yarima Khaled, wanda yanzu shi ne jakadan saudiyya a Amurka, sauran ‘ya’yan gidan sarautar da na koyar sun zabi su gudanar da rayuwarsu a bayan fage.

A yanzu na kan tuna da wannan dan lokacin da na koyar da ‘ya’yan gidan sarautar Saudiyya, inda nake kallon daya daga cikin dalibaina na tasowa a fagen siyasar duniya.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: