Daya daga cikin manyan kwamandojin mayakan Boko Haram, Awwal Ismaila ya mika kansa inda ya tabbatar da cewa shi kansa ya jagoranci mayakan Boko Haram da suka arce da ‘yan Matan Chibok a shekarar 2014.
Ya ce, dalilin da ya sa ya mika kansa ga sojojin Nijeriya sh ne ya gaji da yadda kungiyar Boko Haram ke kashe mutane babu gaira babu dalili inda ya nuna nadama tare kuma da taimakawa sojojin Nijeriya da bayanai game da mabuyan mayakan kungiyar.
Ya kara da cewa yunwa ta addabi sansanonin kungiyar da ke cikin Dajin Sambisa ta yadda a kullum ake samun wadanda ke mutuwa sakamakon Cututtuka.
Ni Na Jagoranci Mayakan Boko Haram Da Suka Arce Da 'Yan Matan Chibok – Auwal

Add Comment