Labarai

Ni Kam Ban Zagi Suruka Ta Ba, Karya Ce Ake Yadawa Akai Na~Inji Sheakh Bello Yabo Sokoto

Fitaccen malami mai wa’azin addinin musulunci dan asulin jihar jihar Sakkwato Sheakh Bello Yabo ya ce shi kam kwata-kwata baida wata alaka kan muryar da ake yawo a kafafen sada zumunta mai nuni da cewar yana zagin surukar sa.

Acikin wani kasaitaccen faifan Bidiyon wa’azin tare da kare kansa kan zargin, Sheakh Bello Yabo ya tuhumi mabiya darikar Shi’a da magoya bayan Sheakh Abduljabbar Nasir Kabara a matsayin wadanda suka shirya masa abun.

Kwanaki Uku da suka gabata dai ne, aka yi yawo da wani faifan Bidiyo wanda aka zaton muryar Bello Yabo ce yana zagin surukar ‘yar sa da diyar ta da kuma mijin diyar sa dake auren jihar Katsina, sai dai malamin ya ce shi kam sam bai da masaniya kan hakan.

Ya kalubalanci wadanda suka kitsa maganar akan su sake sakin wani faifan bidiyo don karyata abunda suka tsara ko kuwa ya dauki mataki.

Fitaccen malamin addinin musulunci na jihar Sakkwato ya bayyana yadda ambaton zagi ko cin zarafi ya yi matsaya a ransa, amma sai dai ya ce baima san an fitar da zagin surukar tasa ba.

Jaridar Sokoto

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: