Ni Atiku Zan Zaba A 2019 – Fitaccen malamin Izala

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya kuma jigo a kungiyar Izala, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya ce dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar zai zaba a zaben 2019.

A karshen makon jiya ne kungiyar Izala a kasar, ta bukaci mabiyanta da su zabi Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, wanda yake neman wa’adi na biyu.

Talla

A tattaunawar da wakilinmu Mustapha Kaita ya yi da Shiekh Sambo, ya bayyana dalilan da ya sa yake goyon bayan Atiku Abubakar.

“Zai zabi mutumin da ya fi taimakon addinin Musulunci da taimakon jama’a da kuma amfanar da mutanen kasa,” in ji shi.

Malamin dai ya bayyana karara cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne zabinsa a 2019.

Talla

Har ila yau, malamin ya yi ikirarin cewa ya kwashe shekara 30 yana tare da Atiku, inda ya ce dan takarar ya “gina masallatan Juma’a fiye da 100.”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

Ana dai ci gaba da samun rabuwar kai a bangaren malaman Izala a Najeriya.

A ranar Asabar ne Kungiyar Izala daya daga cikin manyan kungiyoyin addinin Islama a Najeriya ta ce Shugaba Buhari take goyon baya a zaben 2019.

Shugaban kungiyar na kasa Shiekh Abdullahi Bala Lau ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.

Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, “ya kamata a yi saitin al’ummar Musulmi kan abin da ya kamata.”

“Allah ya kawo saukin rigingimu da tashin bama-bamai dalilin zuwan Shugaba Buhari, illa dan abin da ya rage na fitintinun, Allah zai kawo saukinsu,” in ji Sheikh Bala Lau.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: