Neymar: La Liga ta ki karbar kudin PSg
Wakilan PSG da Neymar sun isa ofisoshin La Liga ranar Alhamis domin biyan Fam miliyan 198 da zai sa Barcelona ta sake shi.
Wata sanarwar da aka aika wa BBC ta ce:
“Za mu iya tabbatar da cewar lauyoyin dan wasan (Neymar) sun zo La Liga domin ba da kudin fansarsa kuma an ki karbar kudin. Wannan ne iya bayanin da za mu iya bayarwa a yanzu.”
Hukumar tana ganin ba zai yiwu ba PSG ta biya kudin Neymar ba tare da take dokokin adalcin ciniki da hukumar Uefa ta kakaba ba.
Add Comment