BBC na neman injiniya mai hada sauti da sauran ayyukan na bangaren fasaha a al’amuran watsa labarai a ofishinta da ke Lagos a kudancin Najeriya.
Wanda ya cancanta zai kasance gwanin bayar da tallafi kan fasaha iri-iri. Sannan zai kasance kwararre wajen magana da kuma rubutu da harshen Inglishi.
Ana kuma bukatar wanda za a bai wa aikin ya kasance wanda ya san yadda ake fitar da bidiyo da sauti daga manhajar hada bidiyo da na sauti.
Baya ga haka, ma’aikacin da ake neman zai kasance mai kwarewa a iya tsara ayyuka da kuma iya kula da gudanarwa cikin matsi da kuma kan lokaci.
Har wa yau wanda ke neman, zai kasance wanda yake iya gabatar da bayanai cikin kalamai kadan ta yadda mutane daban-daban za su gane cikin sauki.
Wanda yake sha’awar aikin, zai iya latsa nan domin samun cikakken bayani game da irin wanda ake nema a aikin.
Kazalika, wanda za a bai wa aikin zai kasance mai iya gani alkaluma daidai yadda ya kamata, kuma ya ci gaba da mayar da hankali kan bayanai.
Masu rike da faafon ECOWAS ko CEDEAO za su iya neman wannan aikin.
Aikin nan aikin na din-din-din ne kuma yana bukatar mutum ya kasance a wurin kullum.
Za a rufe shafin daukar aikin nan ne a ranar 18 ga watan Yulin wannan shekarar.
Add Comment