Hukumar gudanar da jarabawar makarantun sakandiri ta bayyana cewa sun kama dalibai kimanin miliyan 1.2 da laifin satar amsa cikin shekaru bakwai.
– Hukumar ta gano ana barin mafi akasarin daliban su shiga da wayar sadarwa dakin jarabawar
Hukumar gudanar da jarabawar makarantun sakandare ta kasa Najeriya, NECO, ta bayyana cewa sun kama dalibai kimanin 1,283,485 da laifin satar amsa a yayin jarabawar cikin shekaru bakwai.
Sun bayyana cewa dalibai 7,410,030 ne su ka zauna wannan jarabawar daga shekarar 2010 zuwa 2017, kuma a cikin su ne aka kama 1,283,485 da laifin na satar amsa.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, shugaban hukumar gudanar da jarabawar, Farfesa Charles Uwakwe, ya bayyana hakan ne a Birnin tarayya, Abuja, ta bakin wakilin shi a wani taro da aka gabatar na yaki da rashawa a kasar nan.
Wakilin na shi, Dakta Ikechukwu Anyanwu, ya bayyana cewa, a shekarar 2010 ne aka fi samun dalibai masu yawa da aikata wannan laifin, kuma an samu mafi karancin dalibai da suka aikata wannan laifin a shekarar 2014.
Yace, a kwana kwanan nan suka gano cewa, mafi akasarin wadanda ake turawa makarantu don tsaron dalibai wajen yin wannan jarabawa, su na barin daliban ne su shiga dakin jarabawar da wayar sadarwa, wanda mafi yawancin wayoyin na su suna dauke ne da na’ura mai daukon hoto.
Ta wannan hanya ne, daliban suke daukan hoton takardun jarabawar suka aikawa da wasu don su turo mu su amsoshi.
Ya kara da cewa kudin da za a biya na wannan jarabawar bai wuci, N11,350, amma yawancin makarantu suna karbar abinda ya kai N30,000 zuwa N50,000, wanda suna karin kudin ne don wata manufa ta daban wajen aikata rashawa, wanda sanadiyar haka ma yana iya bayuwa da ayi satar amsa.
Source Naij Hausa
Add Comment