Labarai

NCC Ta Karyata Jita-jitar Katse Layukan Waya A Katsina

Daga Sulaiman Ibrahim,
Hukumar Sadarwa ta kasa ta karyata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta inda ya ce hukumar ta umarci kamfanonin sadarwa su rufe tashoshin sadarwar na jihar Katsina kamar yadda ta yi ga makwabciyarta, jihar Zamfara.

Mataimakin Babban Darakta na NCC, Farfesa Umar D. Danbatta, wanda ya yi magana da gwamnatin jihar, ya ce labarin jita-jita ne kawai, karya ne.

Shugaban Hukumar NCC ya kara da cewa wasikar da ake gani tana yawo a kafafen sada zumunta, kofin wacce aka aika zuwa jihar Zamfara ce, inda aka bada sanarwar rufe tashoshin sadarwa gaba daya.

Don haka ya ba da shawarar cewa labaran jita-jitar cewa za a dauki irin wannan matakin a Jihar Katstina ya kamata ayi watsi da batun, saboda ba su fito daga Hukumar ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: