WASU MANYAN LAIFUKAN DA KAN IYA
HANA MACE SHIGA ALJANNA KODA KUWA
TANA SALLAH:-
1) Duk Matar da take da aure tayi zina.
2)Duk Matar da ta mallaki Mijinta ta hanyar
asiri ko ta hanyar tsafi
3)Duk Matar data Hana kishiyarta ta zauna
da Mijinta lafiya
4)Duk matar da ta raba mijinta da
‘ya’yansa, ko ta hanyar asiri ko yaudara
5)Duk matar da ta raba mijinta da ‘yan
uwansa ta hanyar asiri ko yaudara
6)Duk matar da ta yi asiri akan saukarwa
kishiyarta jinin haila duk ranar kwananta sai
haila yazo mata
7)Duk matar da tasa aka daure mahaifar
kishiyarta,don kar ta haihu
8)Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa
mijinta,kuma ta tabbata ba nasa bane
9)Duk matar da tayi daurin baka ga mijinta
don yayi mata kishiya.Ma’anar baka shine:
Duk ranar da zai kwana a dakin kishiyarta
sai ya zamanto bana miji ba.Amma idan ya
dawo dakin matsafiyar sai ya dawo namiji
10)Duk matar da ta nemi mijinta ya
saketa,alhali baya cutar da ita. Kuma ba
yadda ya iya
11)Duk matar da bata godewa mijinta bisa
ga irin abubuwan da yake mata na alkairi
12)Duk matar da take cutar da mijinta da
bakinta
13)Duk matar da batayin wankan janaba,
bayan ta sadu da mijinta,ko batayin wankan
haila ko biki
14)Duk matar da take tona asirin mijinta a
cikin kawayenta
15)Duk matar da take annamimanci
16)Duk matar da take sa kayan da yake
nuna tsiraicinta,irin wanda musulunci yake
fada akan irin shigar yahudawa da nasara
17)Duk matar data kara gashi akan nata
18)Duk matar da tilastawa mijinta yayi mata
wani abu wanda ba zai iya yi ba
19)Duk matar data dauki dan wani ta bashi
Mama (Nono) bada izinin Mijinta ba
20)Duk matar da zata cewa Mijinta tunda
muke dakai meka taba yi mini.
Dukkan wadannan Laifuka guda 20, ko wani
guda daya a ciki, idan Mata ta mutu tanayi
bazata shiga Aljanna ba, koda za ta shiga
sai an babbaka ta.
Allah Yatsare Mu baki daya…
Add Comment