Nasiha

[Nasiha] SHARRI KARE NE

*Sharri Kare Ne*
Da na zo Neman aure Sai da na tabbata na kure adaka wajen samun ‘ya tagari mai mutunci don kauce ma tsautsayi. Amma a ranar da muka tare da Ita bayan an kammala shagulgula, mutane sun watse an bar ni da Ita a cikin gida, na sanya labule na meni abinda da namiji yake nema daga iyalinsa Sai na tarar da Ita ba cikakkiyar ‘ya macce nagartacciya ba. Hankalina ya tashi matuka, na rasa abin da ke yi min dadi a zuciyata. Da farko, saboda kuruciya ba ta fahimci abin da ya sauya min yanayi ba. Amma daga baya ta gane bayan an kwana biyu tana Neman fara’a ga fuskata ta rasa ta. A rana ta Uku Sai da dare ya raba, mu duka mun kasa bacci, sannan Sai ta tashi da durkusa a gabana tana kuka, tana roko na, in rufa mata asiri. Ta rantse min da Allah cewa, yaudarar ta aka yi da sunan aure. A nan ne labarin mutumniyata ya sake yo min sak ga raina. Na hakura na hadiye wannan dafi saboda na San cewa sakayya ce. Wannan ta wuce. Ba mu shekara da iyalina ba Allah ya azurta mu da samun ‘ya Macce. Ina son ‘yata kwarai da gaske. Kuma da kaina na rika kai ta Makaranta tun daga matakin nursery har ta shiga firamari. A lokacin da take Aji biyu, tana ‘yar shekara bakwai kenan, na tafi Ofis Sai wani aiki ya dau Hankalina har na bar Wayata cikin ofis ba fita da Ita ba. Masinjana ya ji ana ta kira Sai ya dauka. Nan take ya rugo ya same ni a firgice ya ce, ana Neman ka a gida. Ko da na buga ma maidakina Sai na ji ta tana ta kuka. Ban tsaya wata-wata ba na dauko makullin mota na sheko gida. Me nake gani? Ga ‘yar nan tawa a kwance cikin jini, wai mai-gadin Gidan makwaucina ya yi mata fyade! Nan take na fadi na suma, ina fadin: “Haka ya isa, ya Ubangiji! Haka ya isa, don girman zatinka ka yafe min”.
  Darussa:
  * Kada ka yi mugunta ga kowa, domin sharri kare ne; mai shi yake bin.
  * Sharrin namiji ya fi karfin Macce, Sai a hada da Addu’a.
  * Ubangiji yana jinkirin sakamakon komai Sai lahira Amma ban da zalunci da ta’addanci a kan wani.
  * Yadda ba ka son barna a cikin Iyalenka, haka su ma mutane ba su so. Don haka ka kame kanka daga iyalan wasu, Sai Allah ya kiyaye maka naka.
Rubutawa :
Haiman Khan Raees 
@HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.