Nasiha

[Nasiha] MAHAIFIYA A MUSULUNCI

*MAHAIFIYA A MUSULUNCI*

   *MATSAYIN MAHAIFIYA A MUSULUNCI*
Mahaifiya itace wacce ta dauki cikin danta, ko ‘yarta, rauni cikin rauni, tundaga daukar cikin izuwa yayewa kimanin shekaru biyu.

 *Mahaifiya* itace ginshiki mai girma a gurin ‘ya’yaye, kuma ita gata agurin ‘ya’yaye.

*Mahaifiya* takan shiga dukkan jarrabawar Allaah, tundaga lokacin da ta dauki cikin danta. *Mahaifiya* takan kasa yin barci saboda kasancewarta a cikin wannan halin, a lokacinda tazo haihuwa kuma anan ne dukkan tsanani abin tausayi da tsoro duka ya tabbata izuwa ga *mahaifiya*.
 
Sautari *mahaifiya* takan shiga hali na damuwa da bakin ciki, akan rashin lafiyan danta, wanda hakan yakan haifarmata rashin bacci.

*Mahaifiyar ka* ce take shayarda kai daga nonon jikinta har zuwa lokacinda a yayeka. Sautari *mahaifiya*  takan kwana da yunwa domin ciyar danta.

  Sau tari *mahaifiya* takan zabi mutuwarta domin rayuwar danta, sau nawa ne *mahaifiya*take bakin ciki akan masifar da ta sami danta??

*Mahaifiya* ce take hakurin jure kazantar kashinka, da harma fitscarinka , wannan duk baya damunta. Itace zata daukeka ta wankeka, tashafa maka mai, tasaka maka tufafinka. Ita ce take shayar dakai ruwa ita ta hakura dakishirwarta.

  Sau nawa *mahaifiya*  take jure jafa’i da rashin kyautatawa da cutarwa dakai danta kake mata, hasalima ita kullun burinta shine Allah ya shiryar da kai, kuma ya datar dakai, cikin dukkan ayyukan Alheri.

To yanzu ko ya dace amatsayinka na wanda ya girma kamanta da duk dawainiyar da *mahaifiyarka* tayi da kai??
    Yanzu kana ganin kafi karfin ka tallafa mata, kasancewar karfinta yayi rauni, koka manta lokacin da kai kake da rauni amma karfinta ya kare acikin hidimar ka??

  Ta yaya zaka kasa biyawa *mahaifiyarka* da ‘yan bukatar da ta nema a gurinka? Ta ya ya za ka kauracewa *mahaifiyarka* alhahli ta raineka a lokacin da bakada mai taimako sai ita??
  Ka kuwa san matsayinka a gurin Allah da Manzonsa??
   Ka kuwa san fushin da Allah ya ke yi ga wanda ya kasa kyautata mu’amalla a tsakaninsa da iyayensa? Musamman ma *mahaifiya*Allah yasa Mu amfana da Wannan Nasiha mai amfani agaremu.AMEEN

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.