Nasiha

[Nasiha] INA IYAYE MASU ZAGI KO TSINUWA GA YARANSU

INA IYAYE MASU ZAGI KO TSINUWA GA YARANSU? 
UMMU FAHAD
Wannan labarin wata Uwa ce da ta yi wa yaronta mugun addu’a.
Tace: Na kasance wata rana ina tsaftace gida sai yarona yazo wucewa lokacin yana karami ya bige wani tangaran na glass ya  fashe.
Sai na fusata dashi, matsanancin fushi saboda tangaran din yana da tsada kuma mahaifiyata ce ta saya min ,ina ta kiyaye shi.
Saboda tsanani fushi nayi masa mugun addu’a nace(Allah ya ruso gini a kanka ya karya maka kasusuwarka)?
Bayan shekaru dayawa na manta nayi masa wannan addu’ar kuma ban San an daukaka addu’ar zuwa sama ba?
Yarona ya girma tare da yan’uwansa. kuma ya kasance nafi tsananin son sa ,kuma yafi min biyayya akan yan’uwansa ,ko kuda bana so ya taba shi.
Ya gama karatu ya samu aiki mai kyau sai na fara nemo masa matar da zai aura.
Mahaifinsa yana da wani tsohon gida babba.sai aka yanke shawarar rushe wannan gidan a sake wani Sabon gini.
Sai yarona ya tafi tare da mahaifinsa zuwa wannan gidan ,kuma ma’aikata suka fara aiki  ana rushe rushe sai yarona ya danyi nisa da mahaifinsa sai wani ma’aikaci ya ruso wani  bangon ginin ba tare da ya lura ba ,sai ginin ya ruso a kan yarona sai kawai muka jii kararsa da ihu sai  muka ji shiru.a nan take aka tsayar da aiki aka dauke  bangon daya ruso masa da kyar aka kira ambulance ya dauke shi,ba su Iya daukan shi cikin sauki ba saboda ya zama kamar fasasshen glass? Suka dauke shi da kyar zuwa asibiti Lokacin da mahaifinsa ya kira ni a waya ya fada min sai na tuna lokacin da nayi masa addu’ar yana yaro.
???nayi kuka mai tsanani har na sume.
Da na farfado sai  na nemi ganin yarona ,da na ganshi sai da nayi nadaamar ganinsa a wannan haalin.saboda gani nayi kamar Allah yana ce min wannan addu’ar ki ce …
na amsa miki bayan lokaci  mai tsawo…… Saboda addu’ar iyaye karbabbba ce.yanxu zan dauke shi daga duniya.
Sai kawai naga numfashin Sa ya dauke ???nayi kuka nayi ihu na ce ina ma zai dawo ya fasa duk tangarayen gilashin da ke gidan..
Kaico na ina ma ban furta wannan addu’ar ba inama ace……ina ma…??.
Kar kiyi saurin yin  mummunar addu’a akan yaranki lokacin fushi.
Ki nemi tsari daga shedan
Ina fada muku wannan sakon hawaye na zuba a idona… ina ma mun mutu tare in huta da radadin mutuwar Ka.
?????????
Kuskuren iyaye kenan  dan Allah idan yaro yayi rashin ji ya fadi ko ya bige ko yaji rauni kar muce masa”
” Allah ya kara””
Sai dai muce Allah ya kare ko ya tsare ko ya kiyaye.
Allah ya tsare  mana yara yayi musu albarka yasa haske a rayuwarsu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.