Nasiha

[Nasiha] HA,INCI

HA’INCI 

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu. 
Hakika a wannan Zamani da muke ciki Ha’inci ya zama ruwan dare Gama duniya! 
A duk inda ka duba Kasuwa, Masana’antu, Makaranta, gidan Aure kai hatta a Masallaci ma yanzu Ha’inci yinsa ake yi a bayyane ma kowa na gani. Haba ‘Yan Uwa na, yanzu Fisabililah ace Musulmi ba zai iya zama da Dan uwansa Musulmi cikin Amana ba sai ya Cuce shi? Wannan Wace Irin rayuwa ce haka? Ashe ba Kamata yayi mu ji tsoron Allah tare da Tausayawa Junan mu ba? 
A wannan zamanin da muke ciki dai abin sai Addu’a. Saboda Lalacewar Al’amura zaka ga wai DA ne da kanshi za’a hada baki da shi a Ha’inci Mahaifinsa. Kai! Wannan Al’amari yana da ban Mamaki. Yanzu in banda Ja’irci da Takadiranci, ace wai da kai za’a hada kai a Cuci Mahaifin ka? Kuma ka yarda? A’uzubillah. 
Wata macen ita kuma, duk lokacin da mijinta zai bata kudin Cefane sai ta Ha’ince shi, in ma kudin ya bar mata sai ta rage, in kuma Canji ne ya rage shi ma shiru kawai kake ji wai maye yaci Shirwa. 
‘Yan Kasuwa ma wasun su suna bata wasu, duk yadda Za’a yi a Cuci mai sayen kaya an sani, a dauko kaya Maras Inganci a siyar musu da Muguwar tsada. Haba ina muke so mu kai kanmu ne? Hatta Dabbobi ma wai sai kaga ana musu Allura don su Kumbura su cika, da ka Siya sai dai ka bige da Yankawa ko kuma suyi Mushe. 
Babban abin Tashin Hankali da Takaici shi ne, yadda wasu kiri kiri Taimakon Masallaci da Jama’a suke Bayarwa domin kara samun Kusanci da Allah, to wadannan kudin da ake Tarawa, su wasu ke Debewa su je su gyara Miyar gidan su, dakin Allah kuma ko oho. Haba wannan Irin Karfin hali har ina?? 
Ya ku ‘Yan Uwa na, ina mai Nasiha a Garemu baki daya da mu dinga kiyaye dokokin Allah, mu rike juna da Amana. 
Allah Ya Azurta mu da kyakkyawar fahimta Ameen. 

Haiman Khan Raees @HaimanRaees 08185819176 

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.