-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Nasiha Ga Tashar Arewa24 Kan Shirin Dadin Kowa


3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nasiha, gyara, gargadi, kira tare da jan kunne, zuwa ga tashar Talabijin na Arewa24.

Daga Abdulhadi Isah Ibrahim.

Gidan TV na Arewa 24, wannan rubutu ne kai tsaye zuwa gare ku, daku da wadanda suke shirya shirin nan na “Dadin Kowa”, hakika gwammai, dubbai da kuma miliyoyin mutane suna kallon tashar ku ta Arewa 24 musamman shirin nan na ” Dadin Kowa”, wannan gidan TV an kira shi da cewa zai rinka raya al-adun Hausawa da kuma dabi’un su da halayyar su har ma da sana’o’in su, kuna kokari wurin nuna al-adu da sana’o’in Hausa kwarai da gaske, amma gaskiya tsakani da Allah kun ci amanar al-ummar Hausawa ta yadda kuka dauko dabi’un Turawan yamma da maguzawan India kuke nuna su a matsayin dabi’un Hausawa.

Na tsaya na kalli programs din ku kusan na awannin rana dana dare, gidan TVn ya kasance wuri ne na koyar da soyayya kawai da kuma wasa da sharholiya, shin Bahaushe bashi da wata al-ada ce sai soyayya kawai? awanni nawa kuka bayar game da addinin Hausawa? watau Musulunci, saboda kusan kashi 97 na wadanda suke kallon tashar Musulmi ne.

Shirin ku na dadin kowa, wani bangare daga cikin sa a yanzu, ya dauki salon ‘kaskantar da addinin Musulunci da kuma Karatun al-qur’ani, ta yanda kuke nuna jahilci da kauyancin duk wanda yake karantar da al-qur’ani da kuma wahalan da yake sha, duk masu kallon shirin sun ga haka kuma sun tabbatar da haka, idan ma kwangila aka baku to ku sani kwangila ce ta yaqi da Allah da manzon sa, wanda tabbas kuna daf da Allah ya rusa ku, ya wulaqanta duk wanda yake da hannu a wannan shiri.

Ni (Abdulhadi Isah Ibrahim) a fahimta ta ma cin amana ne ma da kuka dauki Kalmar (Arewa) kuka sanya wa tashar kuma kuke nuna wannan rashin mutuncin, da ace kun sanya wa tashar suna “Kannywood 24” ta ‘yan diraman Hausa da baza mu damu da wannan rashin kunyar da kuke nuna wa ba da sunan Arewa, amma kunyi amfani da sunan Arewa kuma kuna cin kafar Malaman al-qur’ani na Arewacin Nigeria? baza muyi shiru akai ba, Karatun al-qur’anin nan musamman anan Arewa shine “Nursery school na yaro” shine “Primary school na yaro” tun lokacin da duniya ta fara sanin akwai wasu mutane Hausawa a duniya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25

- Advertisement -

Sannan ina sake zargin ku da cin amanar al-ummar Hausawa ta yanda kuke sanya shirin a lokatan da yara da Matasa suke zuwa makarantar Allo ko kuma ta haddar Al-qur’ani, kamar karfe 8 na dare bayan sallar Isha, ina fadin haka ne saboda ina koyar da dalibai haddar Al-qur’ani a makarantu daban daban, duk ranar da ake da shirin “Dadin Kowa” to makarantar zaka babu kowa musamman yam mata da yara da muke karantar dasu, har wata mata tace mun “Ko za’a dauke karatun ranar da duk ake wannan shirin ne?”, nace mata ” A’a lalacewar mu bata kai haka ba tukun”, mu fifita drama akan littafin Al-qur’ani.

Subsequently Wannan zai jawo ma nayi magana game da shirye shiryen ku irin “Zafafa Goma” da sauran rashin kunya da kuke nunawa, ta yadda kuke gayyato mawaka da makada kuyi hira dasu, kuji matsalolin su, da yanda za’a gyara musu tsiyar su ta kara kyau, Arewa tana cike da Malaman addinin Musulunci na Izala dana Dariqa, awa nawa kuka bayar domin jin ta bakin su game da sha’anin Karatun al-qur’ani da littattafan Hadisi da Fiqhu da harshen Larabci? har a yau Hausawa suna girmama Malaman Musulunci kanana da manyan su, amma baku yi wani tanadi wa wannan ba.

A yau zaka ga mace taqi yin aiyukan da yake cikin gidan mijin ta saboda Dadin kowa, zaka ga yara matasa sun kaurace wa abinda zai amfane su duniya da lahira saboda Dadin kowa, kuma shi Wannan shirin ba wani abu dake da alaqa da addini yake koyarwa ba kai tsaye, babu batun riko da Sallah, tawakkali ko dogaro da Allah acikin sa, sai dai a nuna wa mutum yanda zai samar wa kan sa da mafita idan ya shiga matsala ta hanyar dabarun sa da kokarin sa kawai, sai raha da dariya kawai.

Wallahi idan muka yi shiru akan wannan barnar da kuke watsawa duniya munci amanar al-ummar mu, kuma kuna kara mayar damu baya ne game da addinin mu da tarbiyyar mu, manzon Allah (S.A.W) ya dora al-ummar sa akan shiriya da nagarta ku kunzo kuna warware aikin da yayi a shekaru 23, na rantse da Allah kuna dab da Allah yayi muku hukunci dai dai aikin ku, kuna so ku nuna wa duniya Malaman al-qur’ani basu da daraja, basu da kima, kuma makwadaita ne, to ku sani in ku baku san addinin ba to mu mun sani mun san kariyar da yake bamu, mun san gatan da yake yi mana, lalacewar Hausawa bata kai yadda ku kuke kallo ba.

Wannan jan kunne daga shafin Facebook na (Abdulhadi Isah Ibrahim) zuwa ga Arewa 24 da kuma masu shirya shirin dadin kowa, sannan daga karshe idan har bazai yiwu ku gyara wadannan abubuwan ba ina baku shawari ku canja sunan tashar daga Arewa 24, Kalmar Arewa ta fita daga sunan tashar ku, saboda kuna munana mu a idon duniya wallahi, mu yan Arewacin Nigeria Musulmi.

By……….
Abdulhadi Isah Ibrahim.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: