Nasiha

[Nasiha] BAHAUSHE YALLABAI

BAHAUSHE YALLABAI!
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Wabarakatuhu. Masu iya magana na
cewa “Bahaushe Mai Ban Haushi”,
wannan karin Magana tabbas haka
take, Hakika Bahaushe yana da wasu
Halaye da Dabi’u da suke da Matukar
Ban Haushi da Takaici wadanda sai
dai ace kaico. Watau a yau, da zaku
lura da Yawancin Gidajen Hausawa,
Zaku ga cewa akwai ababen kunya
Makil a cikin wasun su. Bahaushe ne
fa zai auri budurwa Danya Jagab
gwanin ban Sha’awa, Maimakon ya
kula da ita yadda ya kamata bisa
Adalci da Koyarwar Shari’ar
Musulunci sai ya ki, da zarar yaga ta
Ragwabe ta fara fita Hayyacinta sai
yace shi wani auren ma zai karo,
alhalin ga ta gidan nan ma ya kasa
Sauke nauyin ta daya rataya a Wuyar
sa, itama ta biyun dai hakan zai yi
mata, Ho!!! Bahaushe kenan Yallabai!
Shiriritar Bahaushe ba anan kawai ta
tsaya ba, da zarar sun sami wasu
‘Yan Shekaru da matar sa, Shikenan
kuma sai ta koma Ciyar da gidan. Zai
fita bai bata ko sisi ba, bai bar mata
ko Kwayar Masara ba, amma da ya
dawo zai nemi abinci, idan ta kawo
mai, haka Sahoron zai dasa hannu ya
kama ci ba tare da Tambayar ya akayi
aka sami abincin ba. Habaa…
Wannan Irin Hamagwanci har ina???
Wannan dalilin yasa matan Hausawa
da yawa sun fada Barace-barace,
Sace-sace da kuma Yawace-
Yawacen banza domin su sami
abinda zasu rufa wa kansu da
Mazajen su da kuma yaransu asiri. Ni
da ido na naga matar da take…
Domin ta sami kudi, da aka
tambayeta da bakinta tace mijinta ne
baya iya ciyar da ita kuma ko da zai
ji ma sai dai yaji tunda shi yaja. Da
muka bincika kuma sai muka tarar
gaskiya ne abinda ta fada. Ya :Yan
Uwa na maza Don Allah mu dinga
Kokari wajen ganin mun sauke
nauyin da ya rataya a wuyan mu,
domin wallahi duk Irin yadda miji ko
mata suka yi da hakkokin aure to
wallahi zasu yi bayani da Larabci.
Irin wannan mugun hali ne yasa
wasu matan tun da KURUCIYA a jikin
su ma suke Susucewa saboda rashin
kula. Ba ina cewa mata basa laifi
bane, ba kuma cewa nake kada
Mazaje su kara aure ba, amma don
Allah adinga jin tsoron Allah wajen
zama da iyali, a kauda son zuciya a
tsaida gaskiya bisa Sharia. Ina Fatar
Allah Ya Shiryi duk wani mai Irin
wannan halin, Allah Ya fitar damu
daga halin da muke ciki sannan Ya
Zaunar da mu lafiya tare da
Kyakkyawar Fahimta a tsakanin mu
Ameen.
©
Haiman Khan Raees
@haimanraees
January 2017

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.