AUREN WURI 3
Bisa Nazari da Lura dangane da Saurin girma Irin na Mace akan Namiji, da yawan mata Idan har aka ce sai sun gama wannan dogon karatun Tukunna zasu yi aure, to lallai fa an shiga Hakkin su. Domin wata kafin ta gama karatun ta kamo Mahaifiyar ta. Wata kuma kafin ta gama TSARO Ya kwace saboda rudin Shaidan da kuma Tabarbarewar Tarbiyar wannan zamani. Wata kafin ta gama wannan dogon karatun tuni Ni’imar ta da Allah Yayi mata a Matsayin ta na mace sun fara tafiya ta yadda in wani ma ya ganta zai iya tunanin ko Bazawara ce.
Ni a Dan Karamin Tunani na, zai fi kyau a dinga yiwa yara aure a lokacin da ya kamata. Sannan ya kamata iyayen mu su Fahimci cewa, Matukar ka Ilmantar da ‘Yar ka bisa Koyarwar Addinin Musulunci, kuma ka Aurar da ita bisa Sunnah, to shi kenan ka zauna lafiya. Allah ba zai Tuhume ka akan me yasa baka bar Diyar ka ta yi Diploma ko Degree a Medicine ko Nursing ba.
Da Zarar Diyar ka ta gama Sakandare, kuma ka Fahimci cewa ta samu Bokon nan dai dai Gwargwado, sannan ta Fahimci Addinin ta yadda ya kamata, kuma Allah Ya kawo mata Manemi Nagari to me ya rage? Ka Aurar da ita kawai ka Shafawa kanka ruwan sanyi, in yaso ko tana gidan Mijinta taci gaba da karatun idan da bukatar hakan.
Amma barin ta haka nan tana Yawo sai dai wannan yaja nan wancan ya ja can kamar wata rigar Gwanjo, bisa cewa wai ita ai ita Yarinya ce, ko kuma wai ai auren wuri yana Jawowa mata Yoyon fitsari, ko kuma wai sai ta kai wani mataki a karatun Boko ko kuma wani uzuri dai can daban. To ka sani duk wadannan dalilan basu ishe ka hujja a gaban Allah ba Matukar dai ka bar Diyar ka ta Lalace.
Shi kuma wanda ya bar Diyar sa tana Talla alhalin ta isa aure, to Sai dai mu ce INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN domin shi kam yana cikin yanayin da ke bukatar ADDU’A.
Allah Ya Azurta Mu Da Kyakkyawar Fahimta Ameen.
©
Haiman Khan Raees @HaimanRaees [email protected]
08185819176
January 2017
Add Comment