Nasiha

[Nasiha] AUREN WURI 2

AUREN WURI 2
Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu. Ya ku ‘Yan Uwa masu Daraja, ina Fatar kuna cikin koshin Lafiya a duk inda Kuke. Allah Ya sa haka ameen.
A Kwanakin baya nayi wani rubutu mai taken AUREN WURI, inda na bayyana Irin Amfanin da auren wuri yake da shi, Matsayin sa a Addinance da kuma Irin Gudummuwar da rashin yin auren Wurin ke Badawa Wajen wajen rusa Al’umma ta Fuskoki da dama. Sai dai kuma wannan rubutu Nawa ashe ya sosa wa wasu rai ni ban sani ba. Sai daga baya ne Korafin mutane da ya Yi min yawa sai na ankara. Daga cikin masu Korafin, da yawansu sun bayyana min cewa bai kamata ayi wa mace auren wuri ba saboda It’s a Violation of the Human Rights.
To anan ina So ne in Danyi karin bayani dangane da abinda na Fada A baya.
Da Farko dai ina mai baiwa duk wani Wanda na batawa rai sakamakon rubutun da nayi. Sannan ni fa ba cewa nayi kada a bar ‘Ya’ya mata suyi Karatu ba domin mutane da yawa sun yi min korafi akan hakan. To amma abin tambayar anan shi ne, tsakanin karatun Addini Da na Boko wanne Yafi Muhimmanci? Duk wani Musulmi Nagari ya san cewa Karatun Addini shi ne na Farko, daga nan kuma sai na Bokon, kuma duka biyun yana Dakyau a neme su, musamman ga ‘Ya Mace UWAR AL’UMMA!
To amma Fisabililah Iyaye Nawa ne suke Dagewa akan cewa su’ Yar su ba Zata yi aure ba har sai ta Haddace Alqur’ani? Ko Sai ta Kware a Fiqhu?? Ko sai ta goge a karatun Hadisi??? Ko kuma su dage akan cewa Lallai sai ‘Yar su ta kware a wani Fanni na Addini tukunna zata yi aure???
Sannan kuma Iyaye Nawa ne suke cewa su’ Yar su ba Zata yi aure ba har sai ta yi Diploma ko Degree a Chemistry, Physics, Accounting, Biology ko kuma a Sauran Bangarori na karatu??? To idan ka sami Amsar, sai kuma ka dubi Irin halin da Mutanen Yankin da kake suke ciki sannan ka dubi Irin halin da matan kowane bangare dana Ambato a baya suke ciki daga nan zaka gane cewa ashe ana ta rufe kofa da Barawo ne ba’a sani ba.

Zan Ci Gaba In Shaa Allah.
Haiman Khan Raees @HaimanRaees [email protected]
08185819176

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.