AUREN WURI
Assalamu Alaikum WarahmatullAllah Wabarakatuhu.
Auren wuri shi ne yiwa da ko ‘Ya aure tun da sauran Kuruciyar su ko kuma in ce tun suna da Kananan Shekaru. Auren wuri a Musulunce Halal ne domin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wassalam ya auri Sayyida Aisha tun tana da Kananan Shekaru wadanda ba zasu Gaza tara ba duk da yake wasu Malaman sun ce shida ne, ko ma dai nawa ne, abin da dai ya bayyana shi ne, ya aure ta ne tun tana da kuruciyar ta. Kuma lallai da ace yin auren wuri ba Halal bane, to babu yadda Za’a yi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi Hakan. Dalilin da ya sa na fadi haka kuwa shi ne, dukkan wani Musulmin kirki ya san cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam baya kuskure ko kadan. Amma yanzu da yake zamani ya zo, Jahilai sun yawaita kuma masu son zuciya fiye da addini sun bayyana jingim a duniya, sai ga shi ma har an samu masu yin fada da wannan Sunnar ta Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam. Da anyi maganar aure sai kaji sun Ce ai yiwa Yarinyar da bata kai Shekaru kaza ko kaza ba aure cin Zarafi ne domin ya Sabawa Dokar ‘Yancin Dan Adam, kuma wai yiwa Yarinya aure da Wuri na iya kawo mata ciwon Yoyon Fitsari. To anan sai mu ce Dakyau! Munji wannan Bayanin, to amma yanzu kowa ya ga abinda bin irin Wancan Shawarar ya Haifar mana a kasar nan, domin su irin wadannan yaran da ake kin aurar da su da wuri don gudun kada su kamu da cutar Yoyon Fitsari, su ne kuma ake samun su da kwana dakin Samari, Guduwa daga gidan iyayen su su fada duniya, cikin Shege, zubar da ciki, yarda jarirai a bola da sauran Makamantan hakan. Jama’a wannan duk Sharrin Yahudawa da Nasara ne, dama so suke su lalata mu kamar yadda su ma suke Lalatattu. Ku a Matsayin ku na Iyaye ya kamata ace kun sai lokacin da diyar ku ta isa aure, kuma ku aurar da ita a lokacin da ya kamata. Amma Sai kaga wata Shekarun ta Ashirin da doriya amma in anyi maganar aure sai kaji Iyayen ta fa da kansu suna cewa yo duka duka ‘Yar Tamu nawa take?! Hmmm Lallai kam zaku gane nawa take yayin da ido zai raina fata. Wallahi Iyaye ku sani, samun kwanciyar Hankalin ku kawai shi ne ku aurar da diyar ku a lokacin da ya kamata, in kuwa aka tsaya jiran sai tayi Digiri, ko sai mai kudi, ko sai mai Mota, ko kuma wata Hayaniyar can daban har aka samu wata Matsala, to Iyaye ku kuka da kanku. Allah Ya Shirye Mu, Ya kare mu, Ya kuma bamu ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu Ameen.
Rubutawa :
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
Add Comment