Nasiha

[Nasiha] ALLAH SARKI MACE

ALLAH SARKI MACE
Allah Sarki Mace, tun tana cikin Mahaifiyar ta ake juya ta tare da mahaifiyar tata. Idan ta fito duniyar ma haka za’a ci gaba da juya ta yadda ake so. Yayin da ta fara tasawa ma haka za’a ci gaba da juya ta tare da sanyata abubuwa ko tana so ko bata so  hakanan zata yi. Ko a cikin ‘Yan uwanta ma an fi nunawa mazan so akan ta. Da zarar tayi wani abu ko zata yi sai ace “ki bari ke mace ce”  kuma fa an san cewa wannan abun yana da muhimmanci. Hatta idan auren ta ya taso sai ta ci sa’a ma tukun akan bata dama ta zabi wanda ta ke so, in kuma bata ci sa’a ba, hakanan za’a hada ta da wanda bata so, kuma hakanan zata zauna da shi cikin rashin kwanciyar hankali da samun nutsuwa. Idan kuma ta auri wanda ta ke so, to anan din ma tsugune bata kare ba. Dole ne ta tashi da safe ta hada mishi abincin kari, dole ta dafa mai ruwan zafi yayi wanka, sannan kuma ta tsaftace gidan tasa! Bayan ya fita nema, nan ma akwai wata cakwakiyar, ‘yan gyare  – gyaren gida da wanke wanke da goge goge duk suna nan suna jiran ta. Kafin ta ankara sha biyun rana tayi, daga nan kuma sai maganar abincin rana. Haka zata zage damtse don ganin ta kammala akan lokaci. Yamma na karatowa nan ma wani sabon girkin ne ke jiran ta, kuma dole ta sake tsaftace gidan don in mai gidan ya dawo yaji dadi. Kuma dole tayi wanka don mai gida ya ganta da tsafta. Hakanan kuma idan lokaci yayi dole ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta don gujewa fushin Ubangiji. Haka dai abin zai ci gaba da tafiya har ta samu ciki. To daga nan ne kuma abubuwan suke kara Damewa, amma bata da ko da damar yin korafi, to wa ma zata yiwa korafin?  Oh Allah Sarki Mace! Allah Sarki Mace!! Allah Sarki Mace!!! Mace baiwar Allah, mace uwar Al’umma, mace uwar hakuri. Ya Allah ka sakawa matan kwarai da alkhairi, sauran kuma ka shirye su tare da mu Ameen.

Haiman Khan Raees
@HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.