Nasarorin Gwamna El-Rufai A Fannin Gudanar Da Mulki

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Baffah Abubakar

Babu al’ummar da za ta ci gaba sai da shugaba ko shugabanci nagari. Ba za a taba samun shugabanci nagari ba, sai an samu jajirtaccen shugaba nagari. Kyakkaywan jagoranci nagari shi ke kawo cigaban kowace al’umma. Cikin siffofin shugaba nagari, akwai gaskiya da rikon amana, ilimi na addini da zamani, akwai jarinta, hangen nesa da koshin lafiya da sauransu. Wadannan siffofi kuwa Allah ya azurta Malam Nasir Ahmed El-Rufai da su.

Talla

Ganin irin gogewa da ayyukan da Gwamna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya yi a Abuja wanda har gobe ake alfahari da shi, ya sa wasu manyan jihar har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suka ba shi shawaran tsayawa takaran Gwamnan Jihar Kaduna ganin yadda jihar ta zama koma baya cikin sauran jihohin Arewa duk kuwa da kasancewarta Cibiyar Arewa a da.

A yau kuwa ana iya bugan kirji a ce Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmed El-Rufai ta samu dumbin nasarori a shekara uku da rabin da ta yi a kan karagar mulki duk kuwa da matsaloli na matsin tattalin arziki da kasar baki daya ta shiga. Jama’a dai mazauna jihar Kaduna, kai har ma da baki na jinjina wa Gwamnatin Kaduna game da ayyukan da Gwamnatin El-Rufai ta yi kuma take kan yi a Jihar. Ayyuka ne wadanda idanuwa suke gani, kafafuwa suke takawa, sannan kuma kunnuwa ke ji. Wannan ne ya sa wasu ke azanci cewa, “Jama’ar Jihar Kaduna sun zabi Malam, malam kuma ya zabi aiki” . Abin dai sai dai a ce san-barka. Amma wadannan romon demokradiyya da al’ummar Jihar Kaduna suke cin moriya sun samu ne sakamakon irin jajircewa da salon gudanar da mulkin Malam Nasir Ahmed El-Rufai. Wannan ya sa gwamnan daukar wasu tsauraran matakai don dawo da martabar Jihar Kaduna. Wasu daga cikin wadannan matakai da gwamnati ta dauka shi kansa gwamnan sau tari da yawa yana fadi cewa suna da hadari a gare shi amma ya zabi daukan wadannan matakai saboda makomar yaran da ke tasowa da wadanda za a haifa nan gaba.
“Saboda mu inganta rayuwar yaranmu, ya sa muka dauki wasu tsauraran matakai masu hatsari a siyasance. Mun kashe makudan kudade wurin gyaran makarantu. Mun samar da ruwa a makarantu da dama. Sannan kuma yanzu muna gina sababbin makarantu a inda ake bukata.” – Gwamna El-Rufai.

Da zuwan wannan gwamnatin Malam Nasir El-Rufai a 2015 ta dauki matakai da dama don bunkasa kudin shiga a jihar da tsuke bakin aljihun gwamnati, wato takaita kashe kudi a kan abubuwa marasa amfani don samun kudin don kyautata rayuwar al’ummar Jihar Kaduna. Wasu daga cikin wadannan matakai sun hada da:
➢ Gwamna Nasir El-Rufai da mataimakinsa ArcH. Bala Bantex sun zabtare kashi hamsin(50%) na albashinsu, rabi kawai suke karba.
➢ Gwamnatin El-Rufai ta rage yawan kwamishinoni daga 19 zuwa 14.
➢ A ranar 31 ga Watan Agusta, 2015 gwamnatin ta samu nasarar gano Naira biliyan 24 ajiye a asusunan gwamnati daban daban ta hanyar yin asusun bai-daya (Treasury Single Account) wanda suke boye a wasu asusuna da ba a san da su ba, sannan kuma aka toshe wasu kafafen da kudi ke zurarewa.
➢ Gwamnatin ta samu nasarar dakatar da Naira miliyan 221 da ake kashewa duk shekara wurin daukan nauyin mutane zuwa aikin ibadu kasashe masu tsarki.
➢ An samu nasarar gano Naira miliyan 120 da ke tafiya duk wata wurin biyan ma’aikatan bogi a watan Mayu na shekara ta 2015 ta hanyar bullo da sabuwar hanyar tantance ma’aikata na zamani.
➢ An dakatar da duk wani kudi da ake kashewa kan abubuwa marasa muhimmanci a gidan gwamnati da sauran ma’aikatun gwamnati.
➢ Gwamnatin ta samu karin kudin shiga (internal generated revenue) ta hanyar hana biya a hannu zuwa bankuna da kuma ‘POS Machine’ ba tare da an kara wa mutane adadin kudin da suke biya na haraji ba.
➢ Rage yawan kudin da ake kashewa wurin gudanar da mulki: An rage yawan ma’aikatu daga 19 zuwa 14, sannan kwamishinoni daga 24 zuwa 15. Haka kuma kasafin kudin 2015 na gidan gwamnati lokacin PDP kimanin Naira 3 ne amma aka zaftare ya koma Naira miliyan 600.

➢ Sake Fasalin Kananan Hukumomi: Sanya wani kayyadadden adadi na ma’aikatan da kowace karamar hukuma ya kamata ta ajiye inda gaba dayan yawan ma’aikatan kananan hukumomi 23 suka koma 6,896 ban da malaman firamare.
➢ Sake Tsarin Masarautu: Dawowa zuwa tsohon tsarin masarautu kafin shekara ta 2001, aka rage yawan gundumomi daga 390 zuwa 77, sannan yawan dagatai daga 5,882 zuwa 1,429.
• Fara aiwatar da tsarin samar da abubuwan more rayuwa- (SDP 2016-2020) don aiwatar da kudirin Jam’iyyar APC na dawo da martabar Jihar Kaduna. Kaddamar da wannan ya sa aka fitar da wani kundin tsari (SDP Plan 2016-2020). Wannan wani kundi ne da zai yi jagora wurin samar wa al’ummar jihar abubuwan more rayuwa.
• Yin Wani Tsare na Samar da Abuwan More Rayuwa
An kaddamar da wani tsari na yadda za a samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar Jihar Kaduna wanda aka kira da Kaduna Infrastructure Master Plan (KADIMP 2018-2050). Manufar wannan mastafilan shi ne ya magance matsalar karancin abubuwan more rayuwa da jihar ke fama da shi. Ana bukatar kimanin Naira tiriliyon 20 don aiwatar da wannan shirin wanda ake sa ran samun kudaden daga aljihun gwamnati da sanya jari daga kamfanoni da kuma tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25

• Kirkiro Sababbin Hukumomi
An kirkiro sababbin hukumomi a jihar wanda suka hada da Hukumar Zuba Jari da Bunkasa Kasuwanci na Jihar Kaduna da Hukumar Adana Taswira ta Jihar Kaduna (KADGIS), wanda aka daura mata nauyin rijistan gidaje da filaye a zamance don magance rikice rikicen da ake samu daga ‘yan damfara.
➢ Kirkiro Hukumar Tattara Haraji na Jihar Kaduna, wato Kaduna Internal Revenue Service (KADIRS) don maye murbin tsohuwar hukumar tattara haraji ta jihar don tattara haraji a kananan hukumomi 23 a jihar. A shekara biyun farko da kirkiro wannan hukumar, wannan hukuma ta bunkasa kudin shiga na jihar daga Naira biliyan 11 a shekara 2015 zuwa Naira biliyan 23. Sannan kuma Naira biliyan 28 a shekara 2017. Wasu daga cikin wadannan hukumomin sun hada da:
➢ Hukumar Kula da Dokokin Hanya ta Jihar Kaduna, wato KASTLEA
➢ Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna
➢ Hukumar Kula da Shan Miyagun Kwayoyi
➢ Hukumar Kula da Sufuri
➢ Hukumar Samar da Zaman Lafiya
➢ Hukumar Kula da Kaddororin Gwamnati
➢ Hukumar Samar da Ruwa da sauransu

• Sanya Da’a da Bayyana Komai a Faifai Wurin Kashe Kudin Gwamnati
An yi asusun bai-daya, wato Treasury Single Account (TSA) wanda ya taimaka wurin toshe kafofin da kudaden al’umma ke zurarewa zuwa aljihunan wasu tsiraran al’umma. Aka kulle duk wasu asusunan gwamnati da ke bakuna daban daban guda 470, inda aka samu kudi kimanin Naira 24.5 a warwatse a wadannan asusunan.

➢ Fito da sabon tsarin kasafin kudi na Zero-Based Budgeting saboda yadda ake yin kasafin kudi

➢ daidai gwargwado da kudin shi guje wa dogaro da kudaden shiga da jiha ke samu wanda a ba a samun wani kyakkyawan sakamako. Amma wannan sabon tsarin kasafin kudin yana tabbatar an yi kasafin kudi ne daidai bukatuwar al’umma daidai da kudin da jiha ta samu.

➢ An yi sabuwar doka ta bayar da kwangila mai suna Public Procurement Law, 2016 wanda ya sa aka kirkiri hukuma ta musamman mai suna Kaduna Public Procurement Agerncy don tabbatar da an rika bayar da kwangiloli bisa ka’ida ta hanyar tallatawa a jaridu da sauransu.

➢ Gwamnatin Jihar Kaduna ta shiga wani shiri na ‘Open Governance Partnership’, wani shiri ne na kasashen duniya da suka ci gaba inda ake baje yadda ake gudanar da harkokin gwamnati a fili don jama’a su san inda kudadensu ke tafiya kuma a dama da su wurin gudanar da harkokin mulki.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: