Nasarorin Da Na Samu Lokacin Da Nake Shugaban Sojojin Nijeriya, Sun Kai A Rubutu Littatafai A Kai, Cewar Burutai
Daga Comr Abba Sani Pantami
Tsohon hafsin sojojin Najeriya Tukur Buratai, ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki ba irin nasarori da ya cimma, ya ce nasarorin da ya cimma sun kai a rubuta kundin littatafai domin yaba masa a aikinsa.
Tukur Buratai, ya ce ya yi rawar gani yayin da yake kan karagarsa a aikin soja, kamar yadda Jaridar TheCable ta ruwaito.
Da yake jawabi ga manema labarai a karshen mako a Abuja, Buratai ya ce akwai “kundi” na nasarorin da ya samu a Hedkwatar Tsaro dake magana kan kokari a aikinsa.
Ya yi magana ne a wani bikin dare da aka shirya wanda mambobin wata kungiya na Kwalejin Tsaro ta Najeriya ta shirya.
Sai dai fadar shugaban kasar ta bayyana nadin nasu a matsayin tukuici saboda aiki tukuru.