Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya t as ya Gwamnan jihar Edo wanda ya lashe zaben a jiya wato Godwin Obaseki
Kwankwaso ya bayyana hakane jiya ta hannun mai magana da yawunsa a kafafen sada zumunta Saifullahi Hassan.
Kwankwaso yace ina mika sakon taya murna zuwa mai Girma zababben Gwamnan Jihar Edo karo na biyu, mai girma Gov Godwin Obaseki.
Sannan kuma ina taya mutanen Jihar Edo bisa zaben PDP da sukayi kuma suka kare kuri’arsu.
Kwankwaso yace sakon godiya zuwa reshen Kwankwasiyya na jihar Edo da kuma shuwagabanni da yan arewa mazauna Edo bisa kokarinsu a wannan zabe – inji Kwankwaso
Kwankwaso dai shine wanda ya jagoranci jam iyyar sa ta PDP a kanfen din sabon Gwamnan Obaseki A zaben da aka gudanar ranar asabar data gabata.
Add Comment