Nan gaba a yau za a rantsar da Samia a matsayin sabuwar shugaban kasar Tanzaniya
Bayan mutuwar shugaban kasar Tanzaniya John Pombe Magfuli a ranar Laraba, ake sa ran rantsar da Matemakiyar shugaban kasar ta Tanzaniya Samia Sahulu Hassan domin ta maye gurbin shugaba John Magufuli da ya rasu a jiya. Za’a rantsar da ita kuma ta ci gaba da mulki har karshen wa’adinsu 2025.