Labarai

Nan Da Shekaru 2 Masu Zuwa Matasan Jigawa 10,000 Zasu Kasance Masu Noma Dan Riba – Gwamna Badaru

Alh.Muhammad Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da shirin yankan alkama da kuma ba matasa kayayyakin koyan sana’a a garin Gabarin da ke karkashin karamar hukuman Ringim.
Gwamna Badaru Abubakar a jawabin sa, yace gwamnati jihar ta cika Alkawarin ta na Samar da injunanyanka da Chadar shinkafan ga Manila Dake cikin Shirin noma Dan riba sannan kuma zata cigaba da samar da injunan yanka da chasa da kuma sheke shinkafa.
Yace nan da shekaru 2 masu zuwa matasan Jigawa 10,000 zasu kasance masu rike kansu ta hanyar shirin noma dan riba, a cewan sa.
Gwamna Badaru, yace gwamnatin tarayya na kasa ta samarda tan 1,000,000,000 na takin zamani domin sayarwa manoman kasar nan a kudi naira N5,500 akan kowane bahu.
Gwamnan ya kuma ce a yanzu haka gwamnatin jiha ta fara dauko kusan tan 1,000 na kason takin jihar da za’a sayarwa manoma a farashi mai sauki. Inda yace za’a fitar da farashin alkama domin a ba ma manoma kwarin gwiwa.
Gwamna Alh. Badaru ya ce gwamnatin jihar zata Cigaban da ba manoma shawarwari a kai a kai kaman yanda aka saba a kai ta hannun malaman gona da kuma samar musu da ingantaccen iri da taki, magungunan feshe, da duk wani kayayyakin amfanin aikin gona.
Gwamnan ya kuma yi godiya ga alummar jihar a bisa karbar shirin noma gadan gadan kamar yadda gwamnatin tarayya karkashin mulkin shugaban kasa Muhammad Buhari da Gwamnan suka bullo dashi.
Daga bisani gwamnan ya kaddamar da injunan yankan alkama 300 da injunan chasar alkama 20 da kuma na sheke alkama 80.
Kwaamishinan aikin gona da albarkar kasa Alhaji Kabiru Ali a na shi jawabin, yace a mako mai zuwa ne za’a fara rabon takin zamani da ingantaccen iri ga manoman rani.
Martaba sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Abubakar Mahamud yayi amfani da daman da aka ba shi wajen taron ya yabawa gwamnatin jiha bisa bullo da shirin noma dan riba.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.