Najeriya Zata Dawo Da Cigaba Da Fitar Da Ganyen Zobo (zoborodo) Zuwa Kasashen Waje

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Najeriya zata dawo da cigaba da fitar da ganyen zobo (zoborodo) zuwa kasar Mexico.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.

Talla

Wannan bayanin ya fito ne daga hukumar noma mai kula da tanadi da killace tsirrai da albarkatun noma wato Nigeria Agricultural Quarantine Service a turance (NAQS)

Hukumar tayi wannan jawabin ne ta bakin darekta mai kula da tsare-tsare a hukumar wato Vincent Isegbe a lokacin da yake zantawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato NAN a ranar talata

Darektan ya kara da cewar dama an dan dakatar da fitar da ganyen zobon ne na dan wani lokacin sakamakon wasu kwari da suka addabi ganyen da aka tanada domin fitarwa kasashen waje amma yanzu an shawo kan al’amarin

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Darektan ya kara da cewa a shekarar 2017 Najeriya ta fitar da kwantena 1,983 zuwa kasar Mexico kacal inda hakan ya samarwa Najeriya kudin shiga na akalla dalar amurka miliyan talatin da biyar $35m a cikin watanni tara (9) na wannan shekarar

Saboda haka yace yanzu bayan da aka shawo kan dukkanin matsalolin da suka saka aka dakatar da fitar da zobon, yanzu nan da wasu yan satuttuka masu zuwa za’a cigaba da fitar da zobon

Yanzu haka manoman zobon mu sun kagara su fara kuma komai na shirye-shirye ya kammala kuma lokacin fara noman zobon ya gabato za’a fara kowani lokaci daga yanzu

Darektan ya kara da cewar dole ne muyi amfani da wannan damar domin taimakawa wannnan gwaunati maici yanzu wajen kokarinta na sauya akalar tattalin arzikin kasar nan daga dogaro da arzikin man fetur kawai wajen samar mata da kudaden shiga

Daga karshe kuma yayi kira ga manoman Najeriya dasu kara himma wajen noman ganyen zobon domin suma kara samun hanyar samun kodaden shiga na kansu

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: