Labarai

Najeriya za ta yiwa Ahmed Musa gagarumar kyauta bayan kafa tarihi a harkar kwallon kafa

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wa Kyaftin din kungiyar Ahmed Musa kyautar Naira Miliyan Goma (N10m) bayan ya samu nasarar bayyana sau 100 a wasannin kungiyar ta Super Eagle

Musa ya zama na uku daga cikin manyan ‘yan kwallon Najeriya da a tarihi suka fi kowa bayyana, wanda Joseph Yobo da Vincent Enyeama suka bayyana 101, sai kuma shi da ya biye musu baya.

A lokacin da yake shekara 17 a duniya, Musa ya sanya kungiyar ta kwallon kafa alfahari da shi a ranar 5 ga watan Agustan shekarar 2010, a wasan zakarun Afrika wanda aka buga da kasar Madagascar bayan ya karbi hannun Mikel Obi inda suka samu nasarar ci 2-0.

Ya fara zura kwallon shi ta farko a kungiyar Super Eagles a watan Maris din shekarar 2011, lokacin da suka buga wasa da kasar Kenya, bayan bayyanar shi a wasan da suka yi da Cape Verde na zakarun Afrika da za su tafi wasan kofin duniya na 2022, Ahmed Musa mai shekaru 28 a duniya ya samu damar bayyana sau dari a wasannin da kungiyar take hadawa.

Bayan wasan, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya yi alkawarin bawa Ahmed Musa kyautar naira miliyan goma (N10m).

Pinnick ya ce, kamar dai yadda dan jarida Tobi Adepoju ya ruwaito:

Kungiyar NFF za ta bawa Ahmed Musa naira miliyan goma, saboda bayyana sau dari da yayi a wasannin kungiyar. Za mu karrama duka ‘yan wasan mu da suka samu damar bayyana sau 100 daga yanzu.

Ya zuwa yanzu dai Ahmed Musa ya samu nasarar zirawa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kwallaye 15; ya zama dan wasan Najeriya da yafi kowa zira kwallaye a wasan kofin duniya, inda ya zira kwallaye har guda hudu.

Ahmed Musa ya fara zira kwallaye a sabon kulob din da ya koma na kasar Turkiyya
Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle, Ahmed Musa ya shiga kulob din kasar Turkiyya da kafar dama, yayin da ya fara zurawa kulob din kwallaye.

Yayin buga wasan kulob din nashi na Fatih Karagumruk da kulob din Gaziantep, Ahmad Musa ya samu nasarar zura kwallaye, inda suka tashi da ci 3 da 2.

Bayan shafe mintuna 90 a cikin wasan, Ahmed Musa ya samu nasarar zura kwallon da ta yi sanadiyyar hayewarsu a tebur, inda ya yi juya ya yanke ‘yan wasan bayansu guda biyu ya zura kwallon cikin raga.

Kwallon da ya zura a daidai mintuna 90 ita ta basu damar zura kwallaye 3 a ragar su, inda su kuma suke da 1, sai dai sakamakon karin lokaci da aka samu, wasan an tashi 3 – 2.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: