Najeriya Ta Sayi Sabbin Jiragen Yaki 18 Don Yakar Boko Haram

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundunar sojin sama ta Najeriya na jiran isowar wasu sabbin jiragen yaki guda 18 domin yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashi.

Babban hafsan sojin sama na kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce suna jiran isowar jiragen yaki shida masu saukar angulu daga Italiya da kuma wasu jiragen soji guda 12 daga Amurka

Talla

Jaridun kasar sun ambato shi yana tabbatar da haka a yayin bude wani sabon dakin tiyata na zamani a asibitin sojin sama da ke Kano.

Ya ce jiragen za su taimaka wajen murkushe Boko Haram a arewa maso gabashi da kuma masu satar mutane a sassan arewacin kasar.

Tuni ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da ba da kwangilar kera wa Najeriya jiragen yaki guda 12 samfurin A-29 Super Tucano.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Tun a watan Afrilu ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da odar jirajen bayan doguwar tattaunawa da gwamnatin Amurka, matakin da ya kai ga sassauta dakatar da sayar wa Najeriya da makamai.

Ana sa ran kammala aikin kera sabbin jiragen zuwa 2024.

Gwamnatin Najeriya ta ce jiragen za su taimaka wajen karfafa tsaro a kasar da kawo karshen yaki da Boko Haram.

#BBCHAUSA

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: