Dai yana nuni ne da cewa yanzu haka kungiyar likitocin kasar nan masu karatun kwarewa sun fara yajin aikin sai baba ta gani yayin da suka yi fatali da tayin sasancin da gwamnatin tarayya ta yi masau.
Likitocin wadan da ke a karkashin wata kungiyar su mai suna National Association of Resident Doctors watau (NARD) a takaice dai ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kuma rabawa manema labarai.
cewa takardar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Dakta Onyebueze John ta sanar da cewa sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani babban taron da sukayi na shugabannin zartaswar kungiyar a daren jiya.
Shugaban ya cigaba da cewa yanzu haka dai sun sha alwashin ajiye kayan aikin nasu har sai gwamnatin tarayya ta waiwaye su ta kuma cika masu alkawuran da ta daukar masu.
Daga Mikiya Hausa
Add Comment