Labarai

Naira Miliyan 300 Na Marayu Sun Yi Ɓatan Dabo A Asusun Kotun Musulunci A Jihar Kano

Hukumar kula da kotunan shari’ar muslunci ta jihar Kano ta tabbatar da ɓatan wasu kuɗaɗen marayu sama da naira miliyan 300 da ke ajiye a asusun ɗaya daga cikin bankunan da ta ke ajiye kudadenta.

Hukumar ta ce wani bincike da ta gudanar ya nuna cewar an yi amfani da sa hannun bogi wajen fitar da kuɗaɗen daga asusun bankin kotun Shahuci a jihar inda ta ajiye kudaden marayun da ake shari’ar rabon gadonsu a gabanta.

Babban akawun hukumar kula da kotun shari’ar musulunci a Kano, Malam Abubakar Haruna Khalili ya shaidawa BBC cewar kudaden da suke zargin sun yi batan dabo na marayu ne daban daban da ake shari’arsu a gaban kotunan musulunci a sassan jihar ta Kano.

Ya ce an gano ɓatansu ne a lokacin da aka tafi fitar da wasu kuɗaɗe da aka ajiye a asusun bankin na wata shari’a tsakanin wani Ƙwara da wani mutum amma sai aka ce babu kudin a ciki.

“Abin ya rage muna miliyan 9 bayan mun san muna da sama da miliyan 100,” in ji shi.

Ya ce bayan sun lura da wawushe kuɗaɗen, sun sanar da hukumomin yaƙi da rashawa waɗanda kuma bincikensu ya gano kuɗaɗen da suka yi ɓatan dabo sun haura miliyan 300.

Hukumar manyan kotunan na shari’ar musulunci ta ce ba ta san wanda ya wawushe kuɗaɗen ba.

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashwa ta jihar Kano Barista Muhammad Balarabe ya ce za su zurfafa bincike kan wannnan al’amari, kuma za su ci gaba da gayyatar ɓangarorin da abin ya shafa don bayar da bayanai.

Bankin Stanbic IBTC da ake zargin kuɗaɗen sun salwanta a asusun hukumar bai fitar da sanarwa ba kan lamarin kuma ƙoƙarin da BBC ta yi don jin ta bakin bankin bai samu ba.

Yanzu dai abin jira agani shi ne sakamakon rahoton bincike da ɓangarorin biyu za su fitar don gano hakikanin yadda kuɗaɗen suka yi ɓatan dabo da kuma wanda ya wawushe kuɗaɗen na marayu.

-BBC

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: