-Advertisement-


Na Maka Maryam Booth Da Wasu Mutane Da Suka Tayata A Kotu


0 1,519

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Makonni biyu da suka gabata ne dai wani rikici ya balle a masana’antar kannywood tsakanin Maryam Booth da tsohon saurayin ta mawaki Ibrahim Rufai Deezell, inda ake zargin shi da sakin wani bidiyon batanci na jarumar a kafafen sada zumunta wanda har ya janyo aka rika sukar jarumar da masana’antar Kannywood.

Jim kadan bayan billo war wannan bidiyon jarumar ta saki wata wasika a shafin ta na Instagram dauke da rubutun cewa ” Eh gaskiya ne munyi soyayya da mawaki Deezell amma yanzu bama tare kuma shine ya saki bidiyon tsaraicina a duniya, amma zan dauki tsatsauran mataki akan wannan cin mutuncin da ya mun saboda bazan bari ya wuce a banza ba”. Inji Maryam Booth

yuchghghcx

Bayan sakin wannan wasikar da ta yi Shima mawakin ya saki nashi dauke da cewa ” shi bashi da hannun akan cin mutuncin da aka yi wa jarumar yana mai kuma jajanta mata akan wannan iftila’in da ya same ta “. Inji Deezell

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

-Advertisement-

Wannan bai wadatar ba sai kowa a masana’antar Kannywood ya hasala

suka fara daura hotunan jarumar a kafar Instagram su na nuna alhini akan abinda ya faru da ita, wasu daga ciki ma har suna zagin mawakin akan bai kyauta ba kuma zai ga abinda za faru dashi.

Wannan dalilin yasa mawakin ya maka wasu daga cikin mutanen da suka yi masa cha a soshiyal midiya a kotu, inda yake cewa bazai yarda ba akan kazafin da akayi masa kuma sai sun biya shi diyyar Naira million Goma na cin mutuncin sa da akayi.

Kawo yanzu dai bamuji ta bakin jarumar ba akan wannan Karar ta da mawakin yayi a kotu.

#Northflix

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.