Wasanni

Na Koma Karagumruk SK Domin Na Lashe Kofi – Ahmad Musa

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars kuma kaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa, ya bayyana cewa ya koma kungiyar kwallon kafa ta Karagumruk SK ne domin ya taimakawa kungiyar ta lashe kofi kuma sannan ya gamsu da tsarin kungiyar da burin da aka saka a gaba a kungiyar ta kasar Turkiyya.

A yammacin ranar Alhamis Ahmad Musa ya sanar da komawarsa kuniyar ta Turkiyya kuma yanzu ya bar yiwa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wasa tunda ya samu kungiyar da zai ci gaba da bugawa wasa a nahiyar turai.

Tuni dai sabuwar kungiyar da ya koma ta wallafa hoton dan wasan da farin cikin cimma daidaito da shi kuma hakan ya kawo karshen zamansa a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wadda take mataki na uku akan teburin gasar.

“Na gamsu da tsarin kungiyar da kuma irin burin da shugabannin kungiyar suke dashi na ganin nan gaba kadan wannan kungiya ta kai matakin lashe kofuna sannan da samun tikitin kofin turai” in ji Ahmad Musa

Nasarorin da ya samu a Kasashen Rasha da Saudiyya

Musa ya zura kwallaye 11 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 14a wasanni 57 da ya buga wa Al Nassr, tun da ya koma can daga kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a bazarar shekara ta 2018, abin da ya sa suka lashe kofunan Saudi Pro League da Super Cup.

Haka zalika ya yi nasara a kasar Rasha lokacin da ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow inda ya lashe kofunan lig-lig guda uku da kuma kananan kofuna uku, kafin ya tafi kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a watan Yulin shekara ta 2016.

Musa ya gaza taka rawar gani a kungiyar Leicester City inda ya ci mata kwallaye biyar a wasanni 33 sai dai daga baya ya samu matsala da kociyan kungiyar wanda hakan yasa ya koma Saudiyya.

Duk da yake kungiyar kwallon kafa ta West Brom ta kasa daukarsa saboda batun kudi, ana rade-radin cewa Musa zai koma Firimiya Lig ta Ingila ko CSKA Moscow, inda ake matukar girmama shi saboda kwallaye 61 da ya ci mata sanna ya taimaka aka ci kwallaye 33 a wasanni 184 da ya buga.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement