Yawan amfani da shafukan intanet a makarantu da wuraren aiki ya zama wani babban abun damuwa ga hukumomi a Nigeria.
Ana kuma ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan ko ya dace a sa ka`ida dangane da yadda matasa za su dinga amfani da intanet a makarantun, da su kan su ma’aikata a wuraren aikinsu.
Sakamakon shagalar da ake yi daga internet, wasu ma`ikatun ma har sun haramta wa ma`aikata amfani da kuma shiga dandalin sada zumunta a lokacin aiki.
Haka ma hukumar kiyaye hadura ta kasa ta haramta amfani da waya a lokacin tuki don kauce wa hadurran da ke ciki.
Amfani da intanet din dai ya zama tamkar jini da tsoka musamman a tsakanin matasa maza da mata, inda a lokuta da dama kan shafe tsawon dare suna cikin dandalin sada zumunta daban-daban.
Wasu dalibai matasa da suka tattauna da BBC sun ce amfani da shafukan intanet ya zame musu tamkar iskar da suke shaka saboda muhimmancin su a gare su.
Zulaiha Tukur Musa ta ce ta kan shiga shafukan Facebook da Google don ta karanta labaran da abinda duniya ke ciki.
”Bani da ka’idar lokaci, ina yi da rana da kuma dare, na kan yi hira da kawaye na da ‘yan uwana”.
Amfani da intanet in ji wasu daga cikin irin wadannan dalibai yana da shiga rai da ya kan kasance rayuwa bata yiwuwa in babu shi.
Rabi Ibrahim Babina wata matsashiya ce ita ma da ta ce idan wayarta ta samu matsala takan shiga damuwa.
” Kai wayata ta zama babu kudin da zan iya shiga intanet ai na kan shiga wani hali, na gwammace a ce bani da ko kwabo a hannuna.”
Shima dai wani matashi dalibi Abba Ibrahim ya ce, a cikin sa’o’i 24 yana iya sa’o’i 15 yana amfani da shafukan sada zumunta muddin dai akwai waya a hannuna.
Dukkan wadannan dalibai dai sun ce su kan ajiye wayoyinsu ne a lokutan karatu, amma ga wasu ba haka batun yake ba, ko ana karatu su kan saci jiki su leka shafukan na intanet; in ji Dr Ashiru Tukur Haruna, wani malamin jami’a.
Ya ce wannan wata babbar matsala ce musamman idan yana koyarwa sai ka ga wasu dalibai hankulansu ba ya kan darasin da ake koya musu saboda amfani da wayoyin salula suna shiga shafukan na intanet.
A wasu ma’aikatun gwamnati ma haka batun yake, ana kuka da yadda ma’aikata kan shagala wajen amfani da shafukan intanet din da kan kawo cikas wajen tafiyar da al’amura.
Masana dai na ganin cewa idan sharuddan da akan gicciya su yi aiki ba, to takaita shiga intanet din kan iya zama jan aiki.
Bbchausa
Add Comment