Soyayya

Na Kamu Da Soyayyar Farfesa Ahmad Maqari – Zainab Naseer

DAGA Shafin Dokin Karfe TV
Fitacciyar matashiyar nan ƴar gwagwarmaya ƴar asalin Jihar Kano, Zainab Naseer Ahmad wacce ta yi shuhura wajen yin rubuce-rubuce masu janyo cece-ku-ce da tada ƙura a Social Media, ta bayyana cewa a yau ta ji ta kamu da soyayyar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Nageriya, Farfesa Ibrahim Maƙari babban Limami a birnin tarayya Abuja biyo bayan wani bidiyo da malamin ya fitar a shafinsa na Facebook a wannan rana.

Matashiyar ta bayyana a shafinta cewa jin wani abu na alamar kamuwa da soyayyar wani ba abu ne da ya ke faruwa cikin sauƙi a gare ta ba, hasalima aure ba ya gabanta ko kaɗan a halin yanzu, sai dai kuma a yanzun ta yi mamaki da ta ji ta kamu da soyayyar Farfesa Ibrahim Maƙarin har ma ta ji ta na so ta aure shi.

Zainab Nasir Ahmad dai ta yi ƙaurin suna wajen fito da maganganu masu tada hazo a Social Media. Ko da a ƴan kwanakin da su ka wuce ta yi maganar cewa babban burinta a rayuwa shi ne ta ga ta zama shugabar ƙasa ko gwamnar Jihar Kano, kuma ita ce ta taɓa cewa yin aure ba wata nasara ba ce da ɗan adam zai yi alfahari da cewa ya cimma wani buri ba, maganganun da su ka mamaye sabbin kafafen sadarwa aka yi ta tafka muhawara a kansu.

Sai dai kuma a wannan lokaci da ta ƙara bayyana cewa aure ba ya gabanta a halin yanzu amma kuma ba ta san ya aka yi ta ji ta kamu da soyayyar Farfesa Maƙarin ba, mutane sun yi ca akai su na ta tafka muhawara akai wasu na yi mata martani da cewa Malamai dai ba sa barin mata su yi gwagwarmaya saboda haka muddin ta na son auren Farfesa Maƙari sai dai ra watsar da makamanta ta rungumi ibadar zaman aure idan ra shirya, wasu kuma na yi mata martani da cewa aure ta ke so a yanzun duk da a baya ta ce ba wani nasara ba ne. Abin jira dai a gani yanzu shi ne shin ko saƙon zai kai ga Shehin Malamin ?, Wane martani zai miyar a kai, zai yi watsi da buƙatar ko kuwa zai karɓi soyayyar Matashiyar ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: