Labarai

Na kai karar Baba wajen Sarauniya da Firayim Minista -daga Ja’afar Ja’afar

Hausawa na cewa tafiya mabudin ilimi. Haka kuma Dan Anace ya ce na zaune bai ga gari ba.

Wanda bai sani ba zai zata da gaske ne na yi wannan tattaki don na ziyarci Sarauniya Elizabeth a fadar Buckingham da kuma Boris Johnson a gidansa da ke lamba 10 Downing Street. To ba haka ba ne.

—————————-
Sharhi

Akwai wani waje da ake cewa Madame Tussaud’s a tsakiyar birnin London wanda duk wani mutum da ya shahara a duniya za ka ga gunkinsa wanda za ka ga kamar an tsaga kara. A turance su na kiran irin wadannan gumaka “waxworks”. A hakikanin gaskiya babu bambaci a zahirance da shi ainahin mutumin.

Bayan na sayi tikiti kimanin £35 (N25,000), kawai sai na afka. Na shiga wannan daki na fita na shiga wani. Har da wani kogo da na shiga mai ban-tsoro kamar lahira. Akwai wani waje kuma za ka shiga wani karamin tarago ya zaga da kai ka ga yadda aka siffanta mutanen-da da muhallinsu daruruwan shekaru da su ka gabata a birnin London. Haka na yi ta daukar hoto da gunkin mutane iri-iri, tun daga kan Sarauniya, Boris Johnson, Trump, Obama, Churchill, Martin Luther King, kai har da su Rihanna da Kim Kardashian.

Dalilin zuwa na wannan yawo Madame Tussaud’s shi ne don na nusar da mutanenmu da su rika bincika labari ko neman tushensa kafin mu yada.

Yanzu idan da na yi ikirarin cewa na kaiwa Sarauniya ziyara, wani har rantsuwa sai ya maka akan tabbacin hakan. Amma ga mai tunani, abin da zai fara tambaya shi ne: a wanne dalili ne har Jaafar zai samu ganin wadannan manyan mutane shi da ba shugaban kasa ba kuma ba mashahuri ba? Shin me yaru a wajen? Shin me Sarauniyar ta ce? Shin me shafin fadar Sarauniya ya wallafa akan zuwan? Haka ya kamata mu dinga yi don tabbatar da sahihancin labari.

Wannan ba wai yana nuni cewa labarin yaron da Arsenal ta dauka karya ba ne, amma da yawan mu mun yada kafin mu tabbatar da sahihacinsa.

DAGA Manuniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: