Labarai

Na ji dadin yadda na ga Buhari Inji Babban Limamin Landan

– Babban Limamin Landan ya kai wa Shugaba Buhari ziyara

– Faston yace ya ji dadin yadda ya ga Muhammadu Buhari

– Justin Welby yace warakar da Shugaban ya samu ikon Allah ne

Mai magana da yawun-bakin Shugaban kasar Najeriya watau Femi Adesina ya bayyana cewa dazu Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani babban bako.

Babban Faston Kasar Birtaniya Archbishop na Canterbury Justin Welby wanda Aminin Shugaban kasar ne ya taka domin ziyarar Shugaba Buhari. Ba wannan bane karon farko da Limamin ya ziyarci Shugaba Buhari a Landan.

Faston yayi murna da yadda ya ga Shugaban kasar. Welby yace Shugaba Buhari yana samun sauki matuka don tuni har ya murmure sosai. Babban Limamin yace wannan duk ikon Ubangiji ne don shi ke ba da lafiya da waraka.

Dazu mu ka ji cewa Limamin Kalaba za su cigaba da yi wa Shugaba Muhammadu Buhari addua. Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ta faman jinya a Landan ya kuma ji dadin ziyarar wannan Fasto Aminin sa.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.