-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Na Goyi Bayan Haramtawa Jam`iyyata Ta APC Takara A Zamfara -Sanata Marafa


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Na Goyi Bayan Haramtawa Jam’iyyata Ta APC Takara A Zamfara – Sanata Marafa

Shugaban kwamitin albarkatun man fetur na Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Kabir Garba Marafa (Sanatan APC mai wakiltar Zamfara ta tsakiya) ya jinjinawa hukuncin da Babbar kotun tarayya, mai zama a Abuja ta yanke, inda kotun ta marawa INEC baya kan matakin da ta dauka na hana jam’iyyar APC yin takara a fadin Jihar Zamfara.

Idan dai ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne hukumar INEC ta yi watsi da sunayen ‘yan takarar da jam’iyyar APC bangaren gwamnati ta bayar, saboda rashin yin zaben fid da gwani ko cimma matsayar sulhu a tsakanin ‘yan takarar.

Marafa a takardar manema labarai da ya sake a jiya jim kadan bayan hukuncin da Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta yanke, ya ce, hukuncin ya kawo karshen karfa-karfa da kama karyar da gwamna Yari suke yi wa mutane a siyasar Zamfara, wanda hakan zai tilastawa Yari ritayar dole a siyasance.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Babbar kotun tarayyar ta ce, abin da hukumar INEC ta yi, ta yi daidai, domin ba hukumar ba ce ta hana jam’iyyar APC gabatar da zaben fid da gwani a Jihar.

Ita wannan shari’ar ta Babban kotun tarayya da ke Abuja, wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne suka shigar da ita, wadanda suka ce sun samu ne ta hanyar sulhu.

A daya bangaren kuma, Sanata Kabir Marafa ya yi shelar cewa, zai daukaka qara kan hukuncin babbar kotun Jiha ta Zamfara, wacce ke cewa, jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda gwani a Zamfara, wanda APC bangaren Yari suka gabatar.

Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: