MUTUWAR MASU MULKI IZINA CE DA AYA GA ƳAN SIYASA MASU KWAƊAYIN MADAFUN IKO

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abba Yusuf Gidan Fata
Akasarin ƴan siyasa, ƴan boko aƙida da masu madafun iko cikin Gwamnati ba sa kawo mutuwa kusa da su ballantana mutuwar wasu daga cikin su ta zama izina ko aya a gare su.

A cikin watanni uku zuwa huɗu aka yi rashi na mutuwar ƴan majalisun tarayya kusan guda hudu a Nijeriya, dukkan su ba wanda ya san zai mutu balle mutuwar ta masa sallama, kuma shi ma bai san zai mutu ba a cikin wannan lokacin domin ba a shiryawa mutuwa.

Haka mutuwa take kuma tana kan kowa, za ta zo maka, za ta zo min, za ta zo miki, za ta zo muku, za ta zo musu duk lokacin da kwanan mu ya ƙare.

Waɗannan sune ƴan majalisun tarayyar da suka rigamu zuwa gida na gaskiya kamar haka:

1.Late Mr. Suleiman Aliyu Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar lere,jahar kaduna.

2. Late Hon.Yuguda Hassan Kila Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwaram,Jahar Jigawa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 731

3. Late Hon.Muhammad maitala Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Bassa,Jahar Plateau.

4. Late Hon. Muhammad Fagen Gawo Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓaɓura/Garki, jahar Jigawa.

Wallahi duk mai rai mamacine,kuma zai mutu a duk lokacin da baya zato ko tsammani,domin ita mutuwa ba ruwanta da kai yaro ne,babba ko tsaho,kazalika ba ruwanta da kai talaka ne, mai kuɗi ko miskini.

Idan ka shuka alkhairi dole alkhairi ne zai bika har cikin kushewar ka, idan ka shuka sharri, sharrin ne zai ta bibiyar ka har izuwa makwancin ka. Allah ka taimaki zuciyoyin mu wajen aikata alkairi sannan ka hane ta wajen kusantar duk wanni sharri a rayuwa.

Allah ya jiƙan duk wani misulmi, Allah kasa in tamu mutuwar ta zo mu cika da imani.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: