Mutuwar Darakta Aminu Sabo Ta Girgiza Kannywood

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rasuwar fitaccen tsohon daraktan shirin finafinai a Kannywood ta girgiza masana’antar, inda masu shirya finafinan na Hausa kama daga takwarorinsa daraktoci da marubuta, furudusoshi, editoci, masu daukar hoto, jarumai da sauransu su ka bayyana juyayinsu ta hanyoyi daban-daban kan wannan gagarumar rasuwa da a ka yi.

Marigayi Aminu Sabo, wanda ya rasu a ranar Talata ta makon jiya, shi ne daraktan mashahurin kamfanin finafinan nan a jihar Kano, Sarauniya Films, wanda a shekarun baya ya mamaye masana’antar ta Kannywood.

Marigayi Aminu ne ya bada umarni a fitattun finafinai kamar Sangaya, Zarge, Nagari, Sumbuka, Allura Da Zare, Garwashi da makamantansu, wadanda su su ka shuhura a shekarun baya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

Ya rasu ne ranar Talata 20 ga Nuwamba, 2018 da daddare, inda a ka yi jana’izarsa washegari Laraba, kamar yadda tanadin addinin Islama ya zo da shi. Masu ruwa da tsaki da dama na masana’antar sun samu halartar wannan jana’iza.

Haka nan sun yi ta aike wa da sakonnin jimami da ta’aziyya a kafafensu na sadarwa daban-daban. Allah Ya ji kan Darakta Aminu, amin.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: