MUTUWAR ATTAHIRU DA ABOKAN AIKIN SHI: Martani Ga Sista Fatima Aliyu

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Bilya Hamza Dass
Wata mata mai sunan Fatima Aliyu, ta yi wani rubutu mai taken “Hadarin Jirgin Su Janar Attahiru: Boko Haram Da Shi’a Sunji Kunya”. Duk da cewa me rubutun ya kasa fitar da wani dalili da ke nuna wai ƴan Shi’a sunji kunya balle ya alaƙan ta mutuwar da kuma Shi’a, babu mamaki me rubutun be fahimci menene Shi’a da ƴan Shi’a ba, balle azo maganan jin kunya. A cikin duka rubutun me sakin layi 5 babu wata makama sai kame-kame, dan haka ban san ma ta ina zan fara martanin rubutun ba, amma de a hakan bari na fahimtar da masu karatu da bibiya abinda basu sani ba.

Sa farko, akwai tarihin cewa; akwai tsama tsakanin ƴan Shi’a da kuma rundunar sojojin ƙasar nan, wanda ya samo asali ko nace yayi ƙarfi daga watan Disambar shekarar 2015, lokacin da sojojin suka sauka garin Zariya, suka kashe sama da mutane 300 mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky ciki harda ƴaƴan shi

3. Suka ƙona wasu da ran su sannan suka haƙa babban rami suka binne sama da 300 cikin su da yara, mata, da maza, sakataren gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar al’amarin a gaban hukumar binciken JCI. Kuma duka waanna lamarin ya faru ƙarƙashin umurni da jagorancin tsohon shugaban rundunar sojojin kasar Tukur Yusuf Burtai.

Sojojin basu tsaya nan ba, sai da suka kame Shaikh Ibraheem Zakzaky, bayan sun kashe kowa a gidan suka tafi da shi cikin yanayi na rashin tabbas, kafin haka sun rushe makarantar shi, gidan shi.

Wannan dalilin yasa ƴan Shi’a suka doka Burtai a kotun hukunta manyan lefuka na duniya wato ICC. Banda wannan ƴan Shi’a basu da wata matsala da hukumar sojojin ƙasar nan, duk da jinanen su dake wuyayen wasun su, domin hatta cikin sojojin akwai wanda suka nuna rashin kyautuwan abinda ya faru. Suka tausaya tare da barranta kan lamarin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Ƴan Shi’a, basu da wata matsala da marigayi Attahiru na rundunar sojojin kasar nan, domin bayan hadarin jirgin da ya samu ƴan Shi’a sun tausaya har sun masa addu’an Allah ya masa rahama tare da abokan aikin shi.

Tawaga ta musamman ta tashi ƙarƙashin jagorancin ƙanin Shaikh Ibraheem Zakzaky wato Mallam Badamasi suka isa garin Kano domin ta’aziya ga 1 ɗaya daga cikin waɗanda hatsarin Jirgin saman su Attahiru ya shafa wato Iyalan Bargi. Gen. Kulliya. Dan haka muna jan hankalin mutane masu jin daɗin alkalami da su kiyayi rubuta ƙarya da son rai domin manufar su.

Idan su Musulami ne, su tina addini ya koyar da cewa kuyi Adalci domin shi ne yafi kusa da tsoron Allah.

Kuma kada ƙiyayyar ku da wasu mutane su hana ku musu adalci.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: