Labarai

Mutane Bakwai Sun Rasa Rayukansu A Wata Gobara A Jihar Gombe

Rahoto daga gidan rediyon VOA a yau da safe ta bayyana cewa akalla Mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta faru cikin dare a jihar Gombe.
Daraktan ‘Yan kwana-kwana ta jihar Gombe, Solomon Lakwande ya ce, gobarar nan ta samo asali ne daga wutar lantarki, hakan ya biyo bayan binciken da suka yi kuma mutane bakwai ne suka rasa rayukansu.

Ma’aikatar ‘yan kwana-kwana sun ce, domin rigakafin afkuwar irin wannan mummunar gobara, suna wayar da kan mutane ta hanyar amfani da Masallatai da Majami’u da kuma gidajen radiyo, kan cewa mutane su rika kula da duk kayayyakin wutar lantarki, kuma idan za a kwanta a rika kashe duk wasu abubuwan da suka kamata.
Aliyu Haruna, shi ne magidancin da wannan gobara ta yiwa barna, yace gobarar ta tashi ne a gidan amaryarsa yayin da yake can gidan uwargidansa, kasancewar yana da gida biyu kuma a halin da ake ciki a yanzu dai, ya rasa amaryarsa da ‘ya’yansa guda shida.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement