Labarai

Mutane 4 ne suka rasa rayukansu a harin da Boko Haram ta kai kauyen Wanori-Amarwa

A daren Asabar da misalin karfe 11.00 ne Boko Haram ta kai hari kauyen Wanori-Amarwa dake jihar Barno.

Mutane hudu sun rasa rayukansu sannan wasu biyu sun sami raunuka daba dabam.

Idrissa Musa wanda akayi abin a idonsa ya ce Boko Haram sun bi mutane gida-gida a kauyen suna aikata abin da suka ga dama.

Ya kara da cewa Boko Haram sun kwashi buhuhunan abinci sannan sun kuma rusa wasu gidaje.

“Jami’an tsaro sun taimaka wajen kai wadanda suka sami rauni asibitin dake Maiduguri’’.

 

Idrissa Musa ya ce kauyen Wanori-Amarwa dake karamar hukumar Konduga bashi da nisa da wurin da jami’an tsaro ke duba shige da ficen matafiya.

Har yanzu dai sojin Najeriya bata ce komai ba akan harin.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.