Kannywood

Musa Mai Sana'a Ya Nemi Yafiyar Masarautar Kano

Jarumin wasan barkwanci kuma Darakta Musa Mai sana’a ya yi wani Film mai suna ”Masu”, wanda acikin fim din ya hada manyan ‘yan wasa, ciki harda Saratu Gidado (Daso). Amma kuma fim din za’a iya cewa yabar baya da kura. Bisa La’akari da rigingimun da fim din ya janyo. 
Tun farkon fara fim din ake gamuwa da matsala har kawo yanzu da ya kuma gamuwa da wata matsalar. Fim Din ya taba mahibbar masarautar kano, sabida yin amfani da masu biyu da Darakta Musa Mai Sana’a ya yi.
 
Haka Kuwa, ya karya dokar fim bisa kudirinta nakare al’adar hausawa da masarauta.
Sarki Sanusi II ya nuna takaicinsa akan wannan al’amari.
Ganin hakane, yasa Maisana’a da Daso suka nemi yafiyar masarauta akan ta yafe masu, sunyi kuskure wajen yin amfani da masu biyu ba bisa ka’ida ba.