Labarai

Murƙushe Ƴan Bindiga Da Suka Addabe Mu, Shi Ne Babban Burina, Cewar Gwamna Masari

…nan ba da jimawa ba za mu kawo karshen ‘yan bindigar, Cewar Shugaban Sojan Sama
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Kakkabe ta’addanci ta hanyar murkushe ‘yan ta’adda da samar da dawwamammen zaman lafiya ga al’umma shi ne babban kalubalen da ta tasa a gaba kuma take fatar samun nasara, hadin guiwa da jami’an tsaro.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka yau Juma’a, a Abuja, yayin da ya kai ziyarar aiki Hedikwatar rundunar Sojojin sama ta Najeriya.

Gwamnan, wanda babban hafsan mayakan Saman Air Marshal isiaka Oladayo Amao ya tarba, ya kara da cewa wannan ziyara ba ita ce ta farko ko ta biyu ba a jerin ziyarorin da ya kawo ma wannan runduna ba, duk domin samar da tsaro ta hanyar dakatar da ayyukan ta’addanci.

Alhaji Aminu Masari ya bayyana wa Air Marshall cewa, wannan matsala ta faro ne da satar shanu da kuma kisan al’umma nan da can, amma a lokacin da Gwamnati ta dauki matakan dakile satar shanu da kuma yin sulhu da wasu daga cikin barayin shanun, sai abin ya canza salo.

Garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da sauran munanan ayyukan dake keta haddi da mutuncin mutane sukayi kamari. Wannan ya sanya Gwamnatin Jiha ta yanke shawarar ba za ta kara zama da wadannan ‘yan ta’adda ba, idan har suna da bukatar a tattauna dasu, to su nemi jami’an tsaro sannan kuma su nemi aminci da sulhu da mutanen da suke cuta mawa ba dare ba rana.

Ya kara da cewa gudummawa ta sauran tallafi da Gwamnatin Jiha take ba jami’an ba za ta daina, za ma ta iya karawa idan har bukatar hakan ta taso, ma damar al’umma za ta zauna lafiya cikin aminci da kwanciyar hankali.

A na shi jawabin, babban hafsan mayakan saman Air Marshall ya yaba wa Gwamnan a kan irin kai kawon da yake domin samar ma al’umma zaman lafiya. Suna sane da irin muhimman matakan da Gwamna Masari ya dauka yake kuma kan dauka, musamman yanda ya gitta rayuwar shi, ya cikin dazuzzukan da ‘yan ta’addan suke zaune domin yin sulhu tsakanin su da mutanen karkara, duk kuwa da cewa ‘yan ta’addan sun ci amanar wannan sulhu, ga kuma dauki kala kala da Gwamnatin Jihar take baiwa jami’ an tsaro akan kari.

Shugaban Sojan Sama Air Marshal Amao ya bayyana cewa aikin da rundunar ta fara a garin Katsina na kafa mazauni na dindindin wanda ya hada da gina filin safka da tashin jiragen sama yana ci gaba da tafiya, haka kuma aikin karamar tashar jiragen sama da ake yi a garin Funtua shi ma yana tafiya yadda ya kamata kuma a shirye suke domin tabbatar da an kammala su cikin lokaci domin samun damar kai dauki cikin hanzari.

Ya kuma tabbatar ma Gwamna Masari cewa in sha Allah, nan ba da jimawa ba za su dakile wannan matsala da taki ci taki cinyewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: